1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona: An dakatar da lig-lig na Turai

Suleiman Babayo
March 16, 2020

A karshen mako ne aka soke wasanni baki daya kama daga manyan lig-lig na kasashen Turai zuwa sauran wasanni lamarin da ya shafi miliyoyin 'yan kallo da masu sha'awar wasanni.

https://p.dw.com/p/3ZW1b
2. Bundesliga | Greuther Fürth vs. Hannover 96
Hoto: picture-alliance/Ryan Evans

Tuni cutar ta Corona Virus mai nasaba da numfashi ta shafi dubban mutane galibi a China da kasashen Turai gami da sauran kasashen duniya inda ta halaka wasu dubban. 'yan wasa na daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar kuma tuni aka kebe wasu kamar yadda ake yi ga sauran wadanda aka gano ko ake zargi sun kamu da wannan cuta.

Harkokin wasanni na samar da makudden kudi da taimaka wa tattalin arziki kasashe da samar da guraben ayyuka, kuma duk wannan na cikin abubuwan da cutar numfashin ta Coronavirus ke shafa baya ga harkokin lafiya inda dubban mutane suka rasa rayukansu. Sai dai gwamnatoci a kasashen duniya na ci gaba da bin matakan rage radadin cutar gami da fata na samun magani ko rigakafi.

A Najeriya dai wasan dambe na daga manyan abubuwan da su ka samu asali daga al'adun hausawa ba kawai a Arewaci ba har ma da hausawan da ke zaune a kudancin kasar. Yanzu haka dai jihohi da dama na kokarin farfado da wasan dambe, kamar jihar Adamawa da aka shafe shekaru sama da 10 ba'a yi, yanzu aka dawo da shi.