Somaliya: Amirka ta fatattaki 'yan Al-Shabbab
September 13, 2017Talla
Rundinar ta AFRICOM ta dauki wannan mataki ne tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar ta Somaliya a wani yanki da ke a nisan km akalla 260 a Kudancin birnin Mogadiscio inda aka gano maboyar mayakan. Cikin sanarwa da ta fitar a yau Laraba, Rundunar ta Amirka a Afrika ta ce sojojin Amirka za su dauki dukannin matakan da suka dace domin yakar 'yan ta'adda a duk inda suke a Afrika da ma duniya baki daya. A watan Maris ne dai da ya gabata, Shugaban Amirka Donald Trump ya bai wa ma'aikatar tsaron kasar ta Pentagone damar yakar 'yan jihadin na Somaliya a wani mataki na goyon baya ga gwamnatin kasar, inda ake fuskantar matsala ta 'yan Al-Shabbab tun daga shekara ta 2007.