Mariano Rajoy zai ba da sheda a kotu
February 27, 2019Tsohon firaministan kasar Spain Mariano Rajoy, wanda a lokacin mulkinsa yankin Catalonia ya yi yunkuri na ballewa daga Spain zai bayyana a gaban kotu a wannan Laraba don ba da sheda a shari'a mai sarkakiya ta 'yan aware na kasar. Shari'ar da ke zuwa watanni biyu kafin zabuka a kasar.
Rajoy dai ya jagoranci Spain tun daga shekarar 2011 har sai a watan Yuni na shekarar bara da aka kada masa kuri'ar yankan kauna da ta yi awon gaba da kujerarsa saboda batun zargin cin hanci da rashawa dalilin da ya sanya jam'iyyar PP ta masu ra'ayin mazan jiya ta rasa wannan muhimmiyar kujera zuwa ga bangaren masu adawa da ke da ra'ayin gurguzu wato ga Firaminista Pedro Sanchez.
Wannan bayyana ta tsohon Firaminista Rajoy na da muhimmancin gaske kasancewar a lokacinsa ne yankin na Catalonia ya so ballewa daga Spain a watan Oktobar 2017 kamar yadda Farfesa Paloma Roman, masanin kimiyar siyasa a jami'ar Complutense ta birnin Madrid ya bayyana.