Gwamnati ta soki masu zanga-zanga a Spain
October 16, 2019Talla
Wata sanarwa da gwamnatin Spain ta fitar ta caccaki shugabannin 'yan awaren Kataloniya da ke neman cin gashin kan yankin, tare da bayyana su a matsayin wasu 'yan tsirarun da ke son haddasa fitina da tarwatsa hadin kan yankin ta hanyar amfani da hanyoyin tunzura jama'a da su gudanar da tashe-tashen hankula.
A baya an sha yin arangama tsakanin jami'an tsaro da masu bore da zanga-zanga a wasu sassan kasar. Sa'o'i bayan da wata kotu a kasar ta yanke hukuncin shekaru tara zuwa 13 a gidan kurkuku ga wasu jiga-jigan 'yan awaren yankin na Kataloniya, jama'a a yankin Kataloniya sun yi tir da matakin kotu.