Sudan ta janye daga tattaunawar cire mata takunkumi
July 12, 2017Shugaba Omar el-Beshir na Sudan ya sanar da dakatar da duk wata tattaunawa da Amirka kan batun neman dage wa kasar takunkumin tattalin arzikin da aka kakaba wa kasar tasa. Kamfanin dillacin labaran kasar na Suna ya ruwaito cewa shugaban kasar ta Sudan ya dakatar da aikin kwamitin da ya kafa da kuma ke tattaunawa da kasar Amirkar kan wannan batu neman dage wa Sudan takunkumin tattalin arzikin da aka kakaba mata tun a shekara ta 1997.
Wannan na zuwa ne kwana daya bayan da Shugaba Trump na Amirka ya dauki matakin tsawaita wa'adin takunkumin da watanni uku , a daidai lokacin da wa'adi watanni shida da tsohuwar gwamnatin Shugaba Obama ta dauka tun farko kafin yiwuwar janye takunkumin ke shirin kawo karshe.
Amirka dai gitta wa kasar ta Sudan cika sharudda biyar kafin janye mata takunkumin, sharuddan da suka hada da dakatar da taimaka wa kungiyoyin 'yan tawayen Sudan ta Kudu da kuma hada kai da Amirkar a fannin yaki da ta'addanci.