Sudan ta Kudu: Kamen 'yan fafutuka
August 28, 2021
Masu fafatuka a kasar na cigaba da gargadi kan yadda ake murkushe masu sukar lamirin gwamnatin kasar da ke gabashin Afirka. Kamen dai na zuwa ne gabanin zanga-zangar gama-gari da gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasar ta shirya gudanarwa da nufin yin kira ga shugaban kasar ya sauka daga mukaminsa.
A cewar shugaban gamayyar kungiyoyin David Kolok, an kame mutanen ne saboda suna da alaka da su, a don haka ne ya ke gargadin cewa ya kamata a kawo karshen take hakkin jama'a a kasar. Ko da yake rundunar 'yan sandar kasar ta musanta hakan, sai dai kuma ta jibge jami'anta a babban birnin kasar Juba, ta na mai ayyana zanga-zangar a matsayin haramtaciyya, kana ta ce zata hukunta duk wanda ya take dokar da ta sanya.
Kasar Sudan ta Kudu ta sha fama da rikicin siyasa da yunwa da ma matsalar tattalin arziki tun bayan samun 'yancin kanta daga Sudan a shekarar 2011.