Miliyoyin jama'a na cikin tsananin bukatar abinci
February 22, 2019Talla
Matsalar ta kara ta'azzara a sanadiyar tashe-tashen hankula. A ziyararsa a yankunan da yunwa ke yi wa barazana kuwa, daraktan hukumar abinci ta duniya wato FAO, Pierre Vauthier, ya ce lamarin mai tayar da hankali ne, ya kara da cewa, in aka yi sake, kasar za ta fuskanci matsalar fari mafi muni da aka taba samu tun bayan barkewar yakin basasa a kasar.
Yaki ya barke a Sudan ta Kudu a shekara ta 2013, bayan da Shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin yi masa juyin mulki. Mutum fiye da dubu dari hudu ne suka mutu baya ga miliyoyi da suka zama 'yan gudun hijira a sanadiyar rikicin.