Sudan ta Kudu ta hukunta jakadunta
May 17, 2019Talla
Ma'aikatar harkokokin wajen kasar da ke Juba ta ce kawo yanzu ba a san inda wadanda aka kora daga aiki suke ba. Sai dai ta ba da umarnin dakatar biyansu albashi nan take tare da umartarsu su dawo da fasfon jakadancinsu.
Wasu bayanai na cewa gwamnatin Sudan ta Kudu ta rufe ofisoshin jakadancinta a kasashe da dama a shekarun baya-bayannan, sai wasu ma'aikatan ofishin jakadancin na korafin jinkirin biyan albashi.