Sudan ta Kudu ta tura da dakaru zuwa Kwango
April 2, 2023Talla
Kimanin dakarun 45 da suka isa birnin Goma, na daga cikin rundunar hadin gwiwa ta kungiyar kasashen gabashin Afirka da aka kafa a watan Junin bara da nufin wanzar da zaman lafiya a gabashin Kwangon. Ana sa rai nan gaba Sudan ta Kudu ta sake turawa da karin dakarunta kamar yadda ta yi alkawarin aikawa Kwango da sojoji 750 a watan Disambar 2022.
A baya-bayan dai Jamhuriyar Dimokradiyar Kwago na tafka kazamin fada da 'yan kungiyar M23 inda take zargin makwafciyarta Ruwanda da tallafawa 'yan tawayen, zargin da gwamnatin Kigali ta musanta.