Taƙaddama tsakanin China da Japan
December 13, 2012Rikici tsakanin ƙasar China da Japan a kan tsibirin Senkaku, ya ƙara zafafa,bayan da Japan ta sanar da cewar wani jirgin sama bincikke na yaƙi na ƙasar ta China ya keta sararin samaniyarta a karon farkon tun da ricikin ya rincaɓe a cikin watan Satumbar da ya gabata,a lokacin da wani ɓangaran tsibirin ya zama mallakar Japan.
Kakkakin gamnatin ta Japon Osamu Fujimura ya ce sun aike da jiragen yaƙi guda fudu a sansani ,sai dai ya ce babu wata karawa da aka yi tsakanin jiragen na ƙasashen biyu.China ta buƙaci Japan da ta dai'na, gudanar da harkokin a cikin ruwayen da sararin samaniyar tsbirin na Diayou wanda ta ce mallakarta ne.Wannan al'amari ya faru ne a sa'ilin da ƙasar China ke gudanar da bukukuwan nuna juyayi na zagayowar cikkar shekaru 75 da aikata kisan kiasun da Japan ta yi a kan yan China a garin Nankin.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abass