Norwegen Anschläge
July 25, 2011Abin ya zo ne a ba zata, kamar yadda 'yan sandan Norway suke faɗa. Wato dai ana zaton wuta a maƙera ne sai ta ɓilla a masaƙa. Duka-duka abin da aka sani game da mai alhakin kai harin ƙasar Norway ranar juma'ar da ta gaba shi ne mai zazzafan ra'ayi ne da tsananin ƙiyayya ga musulmi. Wannan ta'asar da tayi sanadiyyar rayukan mutane sama da casa'in ta tsorata jama'a a dukkan sassa na duniya kuma ta nunar a fili wani sabon babin da aka shiga na ta'addanci a nahiyar Turai, inda a cikin ƙiftawa da Bisimillah 'yan ta'addan kan halaka mutane masu tarin yawa.
Rahoton mahukuntan tsaron ƙasar Norway dai yana tattare da firgitarwa. Domin kuwa a yayinda a shekara ta 2010 ba a fuskanci wata barazana daga masu zazzafan ra'ayin riƙau ko na gurguzu ba, amma a wannan shekarar ta bana mai yiwuwa lamarin ya rikiɗe ya ɗauki wani sabon fasali. Wannan kalamin ba shakka za a yi masa gyara a cikin rahoton mahukuntan na gaba. Sai dai kuma a haƙiƙa mahukuntan na ƙasar Norway ba su da wata kafa na hana wanzuwar wannan ta'asa, saboda lamarin ya jiɓanci wani mutun ɗaya ne, wanda ko da yake ya saba gabatar da zazzafan ra'ayinsa ta yanar gizo, amma ba ya da wata alaƙa da ƙungiyoyi masu zazzafan ra'ayin riƙau, waɗanda ake da su jefi-jefi a ƙasar ta Norway.
A bisa al'ada dai mahukuntan tsaron na ƙasar Norway suna da cikakkiyar masaniya a game da abubuwan dake faruwa tsakanin waɗannan ƙungiyoyi. Saboda galibi 'yan sanda da jami'an doka ba su fuskantar wata wahala wajen shigar da mutanensu don nemo bayani. Amma dangane da mai alhakin harin na ranar juma'a, mutune da ya ƙallafa wa kansa da kansa tsattsauran ra'ayi ba tare da wata alaƙa da wasu dake da irin ra'ayin nasa ba. Hatta su kansu jami'an tsaron na Norway suna tsoron irin waɗannan mutane. Domin kuwa sakamakon ɓar da kama da wuya mahukunta su samu wata kafa ta tara bayanai game da su ballantana a riƙa bin diddiginsu.
Wani rabo na alhakin harin ke kan 'yan riƙau?
Ayar tambaya a nan dai ita ce, shin wane irin laifi ne za a iya ɗora wa jam'iyyar ƙasar ta Norway mai tsattsauran ra'ayin mazan jiya. Domin kuwa mai alhakin harin yayi shekara da shekaru yana ƙarƙashin inuwar jam'iyyar kuma da yawa daga cikin manufofinsa da ya saba gabatarwa ta yanar gizo na da nasaba manufofinta, abin da ya haɗa har da ƙyamar baƙi. Duk kuwa mai yayata irin wannan aƙida ba shakka zai samar da wani yanayi ne na siyasa, wanda in har rana ta baci, zai kai ga irin wannan ta'asar da aka gani ranar juma'ar da ta wuce.
Mawallafi: Stefan Schölermann/Ahmad Tijani Lawal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar