1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimako ga arewacin Iraki

August 21, 2014

Da yawa daga cikin dubun dubatan mutanen da ke tserewa daga ta'asar 'yan Jihadin IS, sun fada cikin halin rashin tabbas sakamakon rashin kulawa da ta dace.

https://p.dw.com/p/1CygO
Jesiden in Zakho Nordirak 16.08.2014
Hoto: picture alliance/AA

Tsirarru na yankin arewacin Iraki na ci gaba da guje wa tashin hankali da 'yan Jihadi suka haddasa da nufin kafa shari'ar musulunci a kasar. Da yawa daga cikinsu sun fada cikin halin rashin tabbas sakamakon rashin samun kulawa da ta dace. Sai dai wasu kasashen yammacin duniya sun fara taimaka musu da kayan agaji karkashin Majalisar Dinkin Duniya.

Shinkafa da miya ne hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da 'yan gudun hijira take raba wa 'yan Iraki da suka guje wa gidajensu a sansanin da ke garin Dahuk. A halin yanzu dai sama da 'yan arewacin Iraki dubu 80 galibinsu al'ummar Yasidi ne suka nemi mafaka a tsaunukan Sinjar sakamakon rikicin da masu kaifin kishin addini suka haddasa a yankin. Zidan mai shekaru 14 da haihuwa, da kuma iyayensa ke daga cikin wadanda suka tsere wa ta'asar 'yan IS ke haddasawa, cewa ya yi.

"Mu dukkaninmu ne muka kaurace wa gidajenmu, tare da zuwa kan tsaunuka. Mun tare ne karkashin bishiyoyi inda a can muka yi ta kwana. Ba mu da tufafin da za mu sa da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum har lokacin da muka zo nan. A kan hanya, na yi ta ganin mutane na faduwa saboda kishin da ya yi ta damunsu. Sun ta neman mu taimaka musu da ruwa, amma kuma mu ma ba mu da shi."

Kariya a cikin makarantu

A birnin Dohuk dai, wadannan 'yan gudun hijirar na arewacin Iraki sun samu kulawa da ta dace. Da dama daga cikinsu na tsugune ne a tantuna da makarantu da kuma kwarya-kwaryar gidaje da ake gina musu. A garin Zakho da ke kusa da Dohuk da kuma ke kan iyakar Turkiya ma dai, akwai dimbin 'yan gudun hijiran Iraki da aka tsugunar a can. Freya von Groote ta hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi karin haske.

Jesiden in Zakho Nordirak 16.08.2014
Wadannan 'yan Yesidi sun saamu mafaka a garin ZakhoHoto: picture alliance/AA

"Rabin makarantun wannan gari na cike ne makil da 'yan gudun hijira. Wannan yana nufin cewar harkar karatu na tafiyar hawainiya. Saboda da haka ne ya kamata mu samar da mafita. Tabbas ne cewar wadannan mutanen za su kwan biyu a nan gurin."

Babu dai alamun cewar 'yan gudun hijiran Irakin za su iya komawa gida nan da 'yan kwanaki. Dalili kuwa shi ne fada na ci gaba da kamari tsakanin masu da'awar Jihadi na kungiyar IS da kuma Kurdawa da ke neman cire wa kansu kitse a wuta.

Ba dukkanin wadanda yaki ya daidaita a arewacin kasar ne suka samu damar tsira da rayukansu da kuma matsuguni ba. Kusan mutane miliyan guda ne suke gararramba a kan hanyoyi sakamakon tsangwama da suke fuskanta daga masu kaifin kishin Islama. Saboda haka ne a ranar Laraba hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da tsarin taimaka musu.

Jigilar kayan agaji ta sama

Kwanaki hudu za a shafe ana kai kayan agaji daga birnin Alqaba na Jordan zuwa arewacin Iraki. Kayayyakin kuwa sun hada da tantuna da barguna da kuma kayan girke-girke. Sannan kuma wasu ayarin motocin kayan agajin za su taso daga Turkiya da kuma Iran. Adrian Edwards, kakakin hukumar 'yan gudun hijira ta duniya ya bayyana hanyoyin da za su bi wajen yin jigilar kayan agajin.

Irak Hilfslieferungen Frankreich 10.8.2014
Jigilar kayan agaji ta sama zuwa IrakiHoto: Reuters

"Ko ta sama ko ta kasa da ta ruwa. Za mu iya amfani da duk damammakin domin yin jigilar kayayyakin agajin da suke bukata. Wannan taimakon za mu bayar da shi ga wadanda suka fi bukata a yanzu. A yanzu wani rukuni na mutanen ne suka samu matsugunai. Amma kuma za mu rabasu har ga wadanda ba su samu mafaka ba tukuna."

Kasashen Denmark da Jamus da Birtaniya da kuma wasu kasashe na Turai suka samar da kudin da aka saye kayayyakin agajin da za a raba wa 'yan gudun hijiran na Iraki.

Mawallafa: Peter Hille / Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal