Mayar da 'yan mata makarantu a Kenya
December 16, 2015Alkaluma sun yi nuni da cewar daya daga cikin 'yan mata biyar wadanda shekarunsu basu shige 15 zuwa 19ba, tana da ciki ko kuma ta riga ta haihu. Akan haka ne kungiyar da ke sasanta mabiya addinai ta fara wani shiri na sake mayar da 'yan matan da suka haihu makaranta don kammala karatunsu. Mahaifiyarta ta shiga bakin ciki lokacin da ta samu labarin cewar ta samu juna biyu. Chumi wadda ba sunanta na gaskiya ba kenan, yarinya ce da ta samu juna biyu tana da shekaru 16 da haihuwa. Yanzu tana da yaro mai shekara guda da rabi, sai dai ta koma aji domin kammala karatunta:
Ta ce: ''Na samu juna biyu tun ina makaranta, bayan da na haihu sai na zabi in koma makaranta saboda kada rayuwata ta kasance mai wahala"
Ita dai wannan kungiya da ke yanki gaban ruwa na Kenya ta taimaka wajen jan hankalin Iyalin Chumi don su barta ta komka karatu. Mahaifiyar Chumi, Pilly Ramadhan mai shekaru 55, ita ce ke kulawa da yaron Chumi da wasu jikokinta biyu. Bata da aiki don haka ne ma take ganin cewar duniya ta juya mata baya. Maryam Mzee da ke aiki a kungiyar sasanta mabiya addinai daban-daban, ta ce guda daga cikin matsalolin da ake fuskanta a yankin shi ne talauci wanda ke sanya 'yan mata su rika bin maza saboda kwadayin abin hannunsu. Hakan kan kaisu ga yin ciki. Mayar da irin wannan mata makarata kalubale ne babba:
''Iyaye kan ce idan sun koma makaranta wa zai dauki nauyinsu? Mu kan zauna mu tattauna da iyayen inda muke nuna musu muhimmanci da ke akwai na bawa yaran dama ta komawa makarata.''
Maryam na da muradin karfafawa wadannan 'yan mata gwiwa ta yadda za su rika ketare yaudarar da maza ke musu. A kowane mako ta kan ziyarci makarantun gwamnati domin jaddada muhimmancin ci gaba da karatu ga yara mata.