1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsugunne ba ta kare ba kan karin albashi a Najeriya

October 29, 2019

A Najeriya gwamnonin jihohin kasar sun ce ba za su iya bin umurnin gwamnatin tarayya ba game da matakin karin mafi karancin albashin ma'aikata da kasar ta dauka.

https://p.dw.com/p/3S9TF
1. Mai in Nigeria
Hoto: DW

Duk da cewar dai ra'ayi ya zo guda game da biyan sabon mafi karancin albashi a tsakanin gwamnatin tarrayar Najeriya da jihohi, daga dukkan alamu ana shirin raba gari game da batun kare-karen da ke tsakanin manya da matsakaita da ma kananan ma'aikata a jihohin. Gwamnonin kasar da ke cikin matsatsi na kudi dai sun ce gwamnatin kasar ba ta da ikon tsara musu hanyoyi na biyan sabon karin albashin a tsakanin jihohin. Makonni biyun da suka gabata ne dai aka kai ga cimma daidaito a tsakanin gwamnatin tarrayar da kungiyoyin kwadagon kasar game da jerin sauyin da ya kalli kari mai girma ga kananan ma'aikatan tare da rage girmansa tsakanin matsakaita da manyan ma'aikatan kasar. Nasir El Rufa'i dai gwamnan Jihar kaduna da ya ce gwamnatin tarrayar ta wuce makadi cikin rawa a kokari na daidaiton albashin a tsakanin ma'aikatan tarrayar da jihohi.

Nigeria Arbeiterkongress protestiert 2010
Hoto: dapd

Mafi yawa na jihohi na kasar dai sun gaza kaiwa ga biyan tsohon mafi karancin albashin na Naira 18,000 a jihohin, abun kuma da ke nufin jan aiki ga jihohin da mafi yawansu ke tangal-tangal ga bukatu na kudi. Har ya zuwa yanzu dai ana kace-nace tsakanin jihohin kasar da tarrayar ta Abuja game da wani bashin daidaiton lamura. Ana dai sa ran doguwar takaddama da kila ma sabon rikici a tsakanin ma'aikata na jihohin kasar dabam-dabam da ke fatan samun karin mai tasiri ga rayuwa da makoma. To sai dai kuma a fadar Abdullahi Sule da ke zaman gwamnan Nasarawa gaskiya da adalci a tsakanin kowa ne kadai ke zaman mafita ga batun albashin mai rikici.

Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa a tsakanin ma'aikatan na jihohi da ke fatan sauya miya da kuma jihohin da ke fatan daidai kurji iya ruwan da yake iya kaiwa ga fitarwa.