1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan sallamar likitoci a Najeriya

August 15, 2014

Likitoci da sauran jama'a a Najeriya na cigaba da maida martani kan matakin gwamnatin kasar na dakatar da shirin nan na kwarewa da likitoci dubu sha shidda ke yi a kasar.

https://p.dw.com/p/1CvYX
Somalia Mogadischu Kämpfe 15.8.2014
Hoto: picture-alliance/AA

Kwana guda bayan bayyana matsayin da gwamnatin Najeriya ta dauka na soke shirin baiwa likitoci horo don zamowa kwararru, 'ya'yan uwar kungiyar likitocin kasar sun gudanar da zanga-zangar nunin goyon baya ga 'yan uwansu dubu sha shidda da wannan mataki ya shafa.

Kungiyar likitocin da dama ta ke yajin aiki dai ta ce ba za ta koma bakin aiki ba har sai shugaban kasar ya sauya matsayi dangane da wannan lamari da suka ce zai taimaka wajen sake durkusar da harkoki na samar da lafiya a kasar kuma hakan na nufin kawo karshe na kokarin samar da kwararrun likitoci inji shugaban kungiyar Dakta Lawrence Kayode Obembe.

Bombenanschlag auf Kirchen in Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa

Da dama dai na ganin baiken matakin da gwmantin ta dauka a wannan lokaci da cutar Ebola ke cigaba da yin baraza a kasar, wannan ne ma ya sa shugaban kungiyar likitocin Najeriyar da ke neman kwarewa Dakta Jibril Abdullahi ke ganin gwamnatin ba da gaske ta ke ba duba da yadda ta tinkari lamarin musamman ma idan aka dube shi ta fuskar kayan aiki.

To sai dai gwamnatin kasar ta musanta wannan zargi da ake mata na nuna halin ko in kula da batun shawo kan bazuwar cutar Ebola a kasar inda ta ke cewa a tsaye ta ke kan kafafunta wajen ganin ba a fuskanci wata matsala ba kazalika ta ce dakatar da shirin baiwa likitocin horo da ta yi, ta yi shi ne da zuciya daya don ganin ta gyatta tsari na harkokin kiwon lafiya a Najeriya.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Ahmed Salisu