1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama game da samun 'yan matan Chibok

Al'amin Sulaiman Mohammed/ SBMay 20, 2016

An samu rudani dangane da sahihancin yarinyar nan ta biyu mai suna Serah Luka, da Sojojin Najeriya suka ce sun ceto daga sansanin mayakan Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1IrKP
Gangamin ceto 'yan matan Chibok
Gangamin ceto 'yan matan ChibokHoto: DW/K. Gänsler

A ranar Alhamis 19 ga wannan wata na Mayu da muke ciki ne dai rundunar sojojin Najeriya ta bakin kakakinta Kanal Sani Usman Kuka Sheka ta fitar da sanarwa da ke nuna cewa rundunar ta sake ceto daya daga ckin 'yan matan sakandaren Chibok da mayakan Boko Haram suka sace kuma suke garkuwa da su. Sanarwar ta kara da cewa a wani aikin lalata sansanonin mayakan Boko Haram din ne a yankin karamar hukumar Damboa da ke jihar Borno sojojin da kuma matasa 'yan kato da gora da ake wa lakabi da Civilian JTf suka ceto mata 97, kana a cikinsu har da Miss Serah Luka wacce ke a matsayin ta lamba 157 na yan matan da aka sace a Chibok shekaru biyu da suka shude. To sai dai 'yan sa'o'i bayan wannan sanarwa kungiyar iyayen yan matan sama da dari biyu da aka sace a Chibok, sun bayyana cewa Serah Luka ba ta cikin yayansu da ake nema amma sun yi mata murna tare da iyayenta saboda kubuta daga hannun yan Boko haram.

Shekaru biyu da sace 'yan matan Chibok
Shekaru biyu da sace 'yan matan ChibokHoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Yakubu Mkeki shugaban kungiyar iyayen da aka sace yayansu, ya shaida wa DW ta wayar tarho cewa sun bincika sunaye da hotunan yaran da aka sace sannan kuma sun tuntubi mutanen da aka sace musu 'ya'ya ba su samu wata mai wannan suna da sojojin suka bayyana da cewar daya daga cikin yan matan sakandaren Chibok da Boko Haram suka sace ba. Ya kuma kara da cewa bayanan da suka tattara sun tabbatar da cewa yarinyar da sojojin suka gano a ranar Alhamis din 'yar wani Fasto ne da ake zaton an sace ta daga Madagali a jihar Adamawa. Sai dai kakakin rundunar sojojin Najeriya Kanal Sani Usman Kuka Sheka ya tabbatar wa tashar DW ta wayar tarho cewa lallai sun ceto yarinyar ta biyu mai suna Serah Luka a yankin karamar hukumar Damboa a jihar Borno, inda ya ce tabbas yarinyar da dakarunsu suka ceto 'yar makarantar Chibok ce.

Ya zuwa yanzu dai jamaa sun kasa kunne suna jiran hakikanin gaskiyar wannan lamari bayan da bangarori biyu suka bada bayanai masu sabawa juna. A ranar Larabar da ta gabata ma dai sojojin sun bayyana cewa sun ceto Amina Ali daga hannun mayakan Boko Haram wacce iyayen ta suka tabbatar da cewa daya daga cikin yayansu ne wacce kuma aka garzaya da ita zuwa Abuja inda ta gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari. Akwai dai daruruwan mata da yara da ma matasa wadanda mayakan Boko Haram suka sace a sassan jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya.