1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta kori Jakadar Kanada daga kasarta

Abdullahi Tanko Bala
August 6, 2018

Baraka ta kunno kai a dangantakar Saudiyya da kasar Kanada bayan da hukumomin Saudiyyar suka zargi Kanada da yin katsalandan a al'amuran cikin gida na kasar.

https://p.dw.com/p/32fFn
Saudi-Arabien | Kronprinz Mohammed bin Salman
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Jensen

Saudiyya ta kori jakadar kasar Kanada dangane da abin da ta kira katsalandan a al'amuranta na cikin gida.

Hukumomin dai sun baiwa jakadar ta Kanada wa'adin sa'oi 24 ta tattara ya nata ya nata ta bar kasar.

Hakannan kuma Saudiyya ta kira jakadanta a birnin Ottawa na kasar Kanada ya dawo gida.

Kasar ta Saudiyya ta kuma baiyana katse dukkan wasu sabbin zuba jari da kuma cinikayya da Kanada.

Wannan dambarwa dai ta biyo bayan wasu bayanai ne da ministar harkokin wajen Kanada Chrystia Freeland ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta ke cewa Kanada ta yi mamaki yadda hukumomin Saudiyya suka kama Samar Badawi kanwar Ra'if Badawi wani mawallafi a shafin Internet wato Blog a turance wanda ake tsare da shi tare da wata 'yar fafutuka Nassima al Sada.