Takaddamar kasuwanci tsakanin Amirka da kasar Sin
March 23, 2018Cikin kayayyakin da wannan takunkumin ya shafa sun hada da aladu ko namansu, da sauran kayan marmari da karafa da Amirka ke dillancinsu zuwa China, sabon takun saka tsakanin kasashen biyu ya biyo bayan dora kudin haraji da ya kai dala biliyan 50 da shugaba Trump ya sa kan wasu kayayyakin China.
Wannan dai shi ne karon farko da aka samun shugaban kasa a Amirka da ya nuna rashin amincewa da tsarin aiwatar da cin moriyar kasuwancin kasa da kasa tsakanin Amirka da sauran kasashen duniya.
Ganin yadda Donald Trump ya dauki matakin yanke duk wata dangatakar kasuwanci da kuma yin barazanar daukar wasu tsauraran matakai na kange kasarsa daga barazanar da ya ce suke fuskanta, wasu masana na ganin cewa dangantakar kasuwanci tsakanin Amirka da kasashe kamar Turai ta fi gaban gwamnatin Trump. Shugaban na Amirka dai ya ce wannnan mataki nasa zai taimaka domin daidaita al'amuran kasuwancin kasar.
Ma'aikatar kasuwanci da cinikayya ta kasar China ta bukaci Washington da ta sasanta barakar kasuwancin da ke tsakanin kasashen biyu, amma abin ya ci tira.
Tun bayan da ya yi rantsuwar kama mulki shugaba Donald Trump bai yi wata-wata ba wajen sanar da cewa zai fitar da kasar daga cikin wasu yarjeniyoyi kamar yarjejeniyar sauyin yanayi da aka kulla a Paris da kungiyar tsaro ta NATO inda ya soki manufofin gwamnatin da ta shude kan harkar kasuwanci da sauran kasashen duniya, akwai kuma batun gina shinge akan iyakokin kasar da zummar magance matsalar kwararra 'yan cirani da ya ce na matukar haifar da koma baya ga tattalin arzikin kasar, a cewarsa Amirka ce gaba da komai a wajensa kuma ya zaman masa dole ya dauki matakin kare muradun 'yan kasa.
Ana dai ci gaba da kai ruwa rana don ganin shugaban ya mutunta duk wata yarjejeniyar da kasar ta kulla karkashin gwamnatin da ta shude, Trump ya cije kan matakinsa na nesanta gwamnatinsa da bunkasa kasuwanci a tsakanin kasar da kasashen da ake kallo na da matukar mahinmanci, amma kuma masana kamar Gary Schmidzt da Anthony Gardner, na ganin cewa dangantakar kasuwanci tsakanin Amirka da kasashen Turai ta fi gaban gwamnatin Trump