1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya: Ba za mu mika 'yan kasarmu ba

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 10, 2018

Saudiyya ta ce ba za ta mika 'yan kasarta da ake zargi da hannu a kisan dan jarida Jamal Khashoggi ga Turkiyya ba.

https://p.dw.com/p/39mmy
Außenminister Saudi-Arabien al-Jubeir in Kairo
Ministan harkokin kasashen ketare na Saudiyya Adel al-JubairHoto: picture-alliance/dpa/K. Elfiqi

Mahukuntan Saudiyyan dai sun sa kafa ne suka yi fatali da bukatar Turkiyyan na mika mata wasu tsofaffin jami'an gwamnatin Saudiyyan biyu, da take zargi da hannu wajen aikata kisan gilla ga dan jaridar nan dan kasar ta Saudiyya Jamal Khashoggi da aka hallaka a karamin ofishin jakadancin Saudiyyan da ke birnin Santanbul na Turkiyya. Gidan talabijin din kasar Saudiyya na al-Arabiya ya bayyana a shafinsa na Internet cewa ministan harkokin kasashen ketare na Saudiyyan Adel al-Jubair ne ya sanar da hakan. A wata hira da ya yi da manema labarai a Riyadh babban birnin kasar, al-Jubair ya ce kasarsa ba ta mika 'ya'yanta ga wata kasa, a yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa kan bukatar ta Turkiyya.