Take hakkin bil Adama a Yuganda
March 12, 2016Kasar Amirka ta bayyana cewar mahukunta a Yuganda na ci gaba da gallaza wa al'umma da kafafan yada labarai bayan kumbiya-kumbiyar da ta sake kai shugaba Yoweri Museveni kan karagar mulki bayan gwamman shekaru yana mulki.Wannan bayanai da ke fitowa daga Amirka na sake nuna irin tsamin dangantaka da ake samu tsakanin wannan kasa ta Yuganda da kasashen Yamma duk da kasancewarta kawa a garesu a yaki da masu ikirarin Jihadi a yankin Gabashin Afirka.
John Kirby da ke magana da yawun gwamnatin kasar ta Amirka ya bayyana a ranar Jumma'a cewar mahukuntan na kasar Yuganda na ci gaba da kame-kamen 'yan adawa da tozarta magoya bayansu, sannan kasar ta Amirka ta fada wa mahukuntan na birnin Kamapala cewa yin aringizon kuri'u lamari ne da ba shi da gurbi a cikin al'ummar da ke alfahari da dimokradiyya.
A cewar Kirby abin da ke faruwa a Yuganda zai iya bude sabon babi a dangantakarsu da Yuganda abin da kuma zai shafi harkokin tattalinarziki da siyasarsu.