1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun saka tsakanin gwamnati da malamai a Kamaru

Salissou Boukari
October 6, 2017

An shiga wani takun saka a tsakanin gwamnatin Kamaru da malaman makaranta a yankin da ake magana da Turancin Ingilishi inda malaman suka bukaci sauye-sauyen da za su inganta rayuwarsu.

https://p.dw.com/p/2lOSj
Kamerun Schulunterreicht in Moho
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kaze

Dubban malaman makaranta ne suka fantsama kan titunan Yaounde babban birnin kasar a shagulgullan da suka yi na tuni da ranar malaman makaranta, inda suka yi amfani da wannan dama domin sanar da halin da suke ciki na kuncin rashin samun albashi. An rufe makarantu da dama a yankunan Arewa maso Yammaci da kuma Kudu maso Yammacin kasar ta Kamaru inda ake magana da Turancin Ingilishi tun daga watan Nuwamba na shekarar da ta gabata bayan wani yajin aiki da malaman makarantu suka gudanar. Malaman sun nuna adawa da yadda ake son Faransanci ya fi karfi a cikin makarantu da ma gidajen shari'a, sannan kuma ba su da albashi na kwarai.

Wannan al'amari ya jefa harkar ilimi a yankin da ake magana da turancin Ingilishi cikin wani hali domin 'yan makarantar da dama ba su zuwa azuzuwa domin daukan darasi. Masu fashin baki na ganin shugaba Paul Biya ya yi sakaci kann rikicin yankin musanman a wannan lokacin da yara ya kamata su koma karatu suka gagara yin hakan duk da hutu na makarantu ya riga ya kare sanadiyar fargabar iyaye da kuma halin da batun ilimi ya sami kansa a ciki.