1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

'Yan Afghanistan na son Amirka ta fito musu da kudin kasar

December 21, 2021

Sabanin sauran gangamin da sojojin Taliban ke tarwatsawa, a wannan karon jami'an ne suka zagaye masu zanga-zangar suna ba su tsaro don su yi kira ga Amirka ta saki kudaden kasar. 

https://p.dw.com/p/44dfd
Afghanistan Kabul | Protest für Freigabe der eingefrorenen Geldmittel
Hoto: Mohd Rasfan/AFP/Getty Images

Daruruwan masu zanga-zanga a birnin Kabul na Afghanistan sun yi jerin gwanon kira ga Amirka da ta sakar wa kasar kudadenta da ke bankunan ketare da suka kai dala miliyan dubu tara.

 

Masu zanga-zangar rike da kwalaye da aka rubuta '' Ku ba mu kudinmu'' sun tsaya a gaban ofishin jakadancin Amirka da ke Kabul wanda a yanzu yake kulle babu kowa a ciki, suna bukatar Amirka da ta saki kadarorin Afghanistan domin ceto tattalin arzikin kasar da ya shiga mawuyacin hali tun bayan da Taliban ta kwace iko da kasar.

 

Gwamnatin ta Taliban da ta kwace iko a watan Agutsa dai ta kasa samun kudin da za ta biya wa 'yan kasar bukata, lamarin da ya sa gwamnmatin ta talauce, har tafiyar da harkokin gwamnati ke neman zamar mata jidali.