1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban: Ikrarin kwace lardin Panjshir

September 6, 2021

Mayakan kungiyar Taliban da suka kwace mulkin Afganistan sun yi ikrarin karbe ikon lardin Panjshir, yanki daya tilo da ke karkashin ikon dakarun da ke nuna tirjiya ga Taliban.

https://p.dw.com/p/3zxTZ
Afghanistan, Panjshir | Widerstandskämpfer gegen die Taliban
Hoto: Ahmad Sahel Arman/AFP/Getty Images

Zabitullah Mujahid wanda ke zama kakakin kungiyar Taliban ne ya tabbatar da hakan.

Tuni dai aka wallafa hotuna a kafafen yada labarai da ke nuna mambobin kungiyar Taliban tsaye a bakin kofar gidan gwamnan Lardin, sai dai mayakan sun yi watsi da wannan ikrarin kana ana ci gaba da gwabza yaki tsakanin bangarorin biyu.

Ko a ranar Lahadi rahotannin sun nuna cewa, mayakan Taliban sun kashe wata 'yar sanda mai juna biyu a yammacin lardin Ghor. An dai kashe Negara da ke a matsayin ganduroba a gaban mijinta da kuma danta a cewar wani dan rajin kare hakkin bil adama na lardin dake zaune a kasar waje. Kuma tuni wasu tsaffin jami'an yankin biyu suka tabbatar da hakan.