1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban ke tsaron filin jirgin saman Kabul

Abdul-raheem Hassan
August 31, 2021

Amirka ta kawo ƙarshen mamayar da ta yi na kusan shekaru 20 a Afghanistan bayan kammala janye dakarunta daga filin jirgin saman Kabul

https://p.dw.com/p/3zk0u
Afganistan, Flughafen in Kabul
Hoto: Wakil Kohsar/AFP/Getty Images

Sao'i kafin cikar wa'adin kammala ficewar sojojin Amirka daga Afganistan a wannan Talata, a daren Litinin jirage masu saukar ungulu sun dauki ragowar dakaru daga filin jirgin saman Kabul. Wannan dai na zuwa ne bayan makonni biyu da sojojin suka yi suna kare filin tashin jirgin daga dubban sojoji 'yan Afganistan da ke neman tserewa daga kasar bayan da Taliban suka karbe iko da gwamnati. Sai dai sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya ce kasarsa za ta fara sabon babin hulda da Afghanistan.

"Kwanaki goma sha takwas da suka gabata, Amirka da kawayenta sun fara aikin kwashe mutanensu daga Kabul. Kamar yadda ku ka ji daga Pentagon sao'i kadan da suka gabata, an kammala aikin. Fiye da mutane 123,000 aka fitar da su lafiya daga Afghanistan. Wannan ya hada da Amirkawa kusan 6000. Wannan ya kasance babban aikin soja, diflomasiyya da ayyukan jinkai. Wannan shi ne aiki mafi wahala a tarihin ƙasarmu, kuma abin ban mamaki na dabaru da dai-daitawa a  yanayi  mawuyaci da ake iya tunani."

US-Präsident Joe Biden hält in Washington eine Rede über Afghanistan
Hoto: Jonathan Ernst/REUTERS

Shugaba Biden ya ce kwamandojin sojoji baki daya sun yi maraba da kawo karshen kwaso jama'ar kasar daga Taliban ba tare da neman karin wa'adi ba. Ya kuma umarci sakataren harkokin kasar Blinken ya dai-daita tare da abokan huldar kasa da kasa wajen ganin Taliban sun mutunta alkawarinsu na amintacciyar hanya ga Amirkawa da sauran waɗanda ke son barin Afganistan cikin ruwan sanyi.

"Na farko, mun gina sabuwar ƙungiya don taimakawa jagorancin wannan sabuwar manufa. Ya zuwa yau, mun dakatar da huldar diflomasiyyar mu a Kabul kuma muka tura ayyukan mu zuwa Doha, Qatar, wanda nan ba da jimawa ba, za a sanar da shi ga Majalisa. Ganin yanayin rashin tsaro da ba a tabbatar da shi ba da kuma yanayin siyasa a Afghanistan, matakin hankali ne da za a ɗauka. Za mu ci gaba da kokarin da muke yi na taimaka wa Amurkawa, 'yan kasashen waje da 'yan Afghanistan barin Afghanistan idan sun zabi hakan."

Afghanistan | US Militärflugzeug startet am Flughafen Kabul
Hoto: Aamir Qureshi/AFP/Getty Images

Akalla sojojin Amirka 2,400 ne suka mutu a tsawon shekaru 20 na yakin da Amirka ta shiga a Afghanistan, na baya-bayan nan shi ne harin kunar bakin wake da aka kai a ranar 26 ga watan Augusta da ya kashe sojojin Amurka 13 da wasu 'yan Afghanistan 169 baya ga mutanen da jirage suka taka. 

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a ranar Talata ta ce bude filin jirgin saman Kabul yana da "muhimmancin gaske", yayin da yanzu kasashen yammacin duniya ke tunanin yadda za a fitar da karin mutane daga Afghanistan bayan kawo karshen tashin jiragen da Amurka ke jagoranta. Su ma a nasu bangaren Taliban sun jadda alkawarin cewa ba za ta zama barazana ga duniya ba yayin karbe iko da filin jirgin Kabul. Zabihullah Mujahid, shi ne mai magana da yawun kungiyar Taliban.

"Wakilin jama'ar Afghanistan, Masarautar musulunci ta Afganistan ta na son samar da kyakkyawar alaƙa da duniya, da yin alaƙar diflomasiyya mai ƙarfi da kwanciyar hankali tare da duniya, ciki har da Amirka, kuma muna son dai-daita dangantakarmu da Amirka a nan gaba."

A ranar 15 ga watan Augustan 2021 ne mayakan Taliban suka shiga birnin Kabul tare da karbe iko, bayan da sojojin Afghanistan suka mika wuya, matakin da ya sa tsohon Shugaban kasar Ashraf Ghani ya tsere daga babban birnin kasar.