1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe jami'in tsaro a Afganistan

Abdul-raheem Hassan
August 23, 2021

Rahotanni daga Afghanistan na cewa an kashe daya daga cikin dakarun kasar, wasu uku sun jikkata sakamakon barin wuta tsakanin jami'an tsaro da wasu 'yan bindiga dadi a wajen filin jirgin saman birnin Kabul.

https://p.dw.com/p/3zNkX
Indien | Evakuierte Afghanen aus Kabul
Hoto: IANS

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da mayakan Taliban suka gargadi Amirka ta yi kuka da kanta idan ba ta kammala janye sojojinta ba a karshen watan Agusta, amma Shugaban Amitka Joe Biden ya ce yana kan bakarsa na kwashe dukkannin 'yan kasar daga Afganistan zuwa gida kamin karshen wa'adin ya cika.

Tun bayan da Taliban ta karbe iko da kasar Afganistan, manyan kasashen duniya ke cikin rudanin kwashe mutanensu, sai dai kasashen kungiyar Tarayyar Turai EU da Amirka na cewa da wuya a iya kashe kowa da kowa saboda halin da ake ciki na rashin tabbas a filin jirgin saman Kabul.