Taliban ta fara sukar Amirka
August 22, 2021Wani jami'in Taliban mir Khan Mutaqi ya sanar a wannan Lahadi cewa abin mamaki ne ace duk da karfin ikon da Amirka ke da shi a duniya amma ta kasa kawo daidaito a filin jirgin saman Kabul. Jami'in na Taliban ya ce a cikin sassan kasar Afghanistan akwai zaman lumana, filin jirgin saman Kabul ne kawai ke cikin rudani.
Batun kwashe mutanen dai na ci gaba da daukar hankulan mutane, inda a baya-bayan tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya soki Shugaba Joe Biden da yi wa Amurka abin kunya a sabili da kwaso mutanen da ke cikin hadari a Afghanistan. Haka ma dai lamarin yake a nan Jamus, inda wasu ke nuna rashin jin dadinsu kan yadda Jamus din ta nuna kasala wurin kwaso mutanenta a kankari.
Ma'aikatar tsaron Amirka ta Pentagon ta ce kawo ranar Asabar mutane 17,000 aka kwashe daga Kabul tun bayan da Taliban ta kwace iko da kasar.