COVID-19: Talakawa ba su gani a kasa ba
April 8, 2020Kama daga Kwali da ke Abuja ya zuwa garuruwa kamar Jalingo a jihar Taraba da sauran sassan kasar daban-daban dai, ma'aikatar jin kai da agajin gaggawa na fadin tai nisa, a kokari na tallafawa al'ummar da ke ji a jikinsu sakamakon dokar zaman gida da nufin kaucewa yaduwar COVID-19. To sai dai kuma rikici na neman ballewa tsakanin talakawa na kasar da ma wakilansu a majalisun kasar guda biyu da ke fadin taimakon ya bi ruwa kuma bai kai ga talakawan da ake fatan sauya rayuwarsu a yanzu ba.
Talakawa cikin tsaka mai wuya
Usman gambo dai na zaman wani dattijo dan shekaru 72 da kuma ya shaidawa DW ta wayar tarho cewar, har yanzu yana zaman jira na agajin a garin Gwagwalada, amma kuma bai kai ga samun nasara a burin nasa ba yana mai cewa: "Ba ni da abun da zanci yanzu balle na an jima, sannan kuma ga marayu, 'yata ce mijinta ya rasu ya barmun. In na kalle su kuka nake. Wallahi har yanzu da nake maka magana ban karya ba ina jira in dan yi wata dabarar, amma ban karya ba. Sabo da haka ina rokon wannan mata ta yi amfani da matsayinta ta taimaka mana.
Duk da cewar dai an rika nuna masu amfana daga agajin ta gidan talabijin mallaki na gwamnatin kasar, jam'iyyun adawar kasar sun ce ana siyasa da agajin da ke karkata zuwa magoya bayan jam'iyya mai mulki.
Yiwuwar bijirewa doka
To sai dai kuma a fadar Hajiya Fatima Goni da ta jagoranci wata kungiyar magoya baya ta shugaban kasar a zaben da ya shude, tallafin na gwamnatin kasar bai isa hannusu ba. Ko baya na magoya baya dai su kansu 'yan majalisun kasar da ke zaman wakilan al'aumma sunce masu tallafin na rawa da kidansu ne ba tare da tunanin zahirin da ke cikin kasar a halin yanzu ba, a fadar Mansu Ali Mashi da ke zaman dan majalisar wakilan kasar daga Katsina. Tuni ma dai a wasu wuraren 'yan kasar suka fara nuna alamun bijirewar umarnin 'yan mulkin, bayan barazanar fadawa a cikin yunwar da ke wucewa da sanin hatsarin COVID-19 a garesu.