1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

110508 Birma Hilfe

Zainab MohammedMay 11, 2008

Kokarin tallafawa Burma na fuskantar tsaiko

https://p.dw.com/p/Dy8l
Tallafin Ruwan ShaHoto: AP

Gwamnatin mulkin sojin ƙasar Burma na cigaba da haifar da tsaiko a kokarin da ƙungiyoyin bada agaji da ƙasashe keyi,na kai ɗaukin abinci da kayyayakin agaji wa mutane million 1 da dubu 500 dake bukatar wannan tallafi.

ƙasashen duniya da wasu ƙungiyoyin agaji na kasa da kasa na muradin ganin cewar sun tallafawa al'ummomin ƙasar ta Burma adangane da wannan mahaukaciyar guguwa data jefa mutane kimanin miliyan 1 da dubu 500 cikin halin neman taimako.Gwamnatin mulkin sojin Kasar dai tace a shirye take na karban dukkan tallafi daga waje,amma bazata amince wa masu rarraba kayayyakin na ketare suyi yawo cikin Burma ba.

Jakadan Burma a Majalisar Ɗunkin Duniya Kyaw Tint Swe yace suna maraba da duk wani taimakao daga ketare...

"Muna kokarin gaggauta faɗaɗa rarraba kayayyakin tallafi a sassa daban daban da wannan guguwa ta ritsa dasu,mun godewa dukkannin kasashe da ƙungiyoyi da suka bawa mutanemmu taimako.Muna kuma anan zan jaddada cewa muna marhabin da tallafi daga ko'ina"

Wadanda suka ganewa idanunsu halin da ake ciki a yankunan kudancin Burma da wannan mahaukaciyar guguwa ta auku,musamman a yankin DElta na Irrawaddy,sunce dubban mutanew n a cikin halin ni 'yasu.Wani Ɗan jarida daya ziyarci wani asibin dake yankin yace yara da mata da mazaje na zube na kasa domin babu wurin kwanciya,balle wuta .....

"halin mawuyaci da jama'a ke ciki ya fi karfin a kwatanta.Akwai marasa lafiya masu yawan,gashi babu isasshen kulawa da tallafi.Dukkannin mutanen na bukatar ruwan sha mai kyau,da abinci,da magunguna dama tsabtace kewayen,inda suke zama"

Kawo yanzu dai kididdigan MDD na nuni dacewar akalla mutane dubu 100 ake zargin sun rasa rayukansu.Kuma Idan ba gaggauta kai ɗauki akayi wa marasa lafiya dake jinya ba ,za a iya samun karuwan yawan waɗanda suka rasa rayukan nasu,saboda rashin kulawa.

Kungiyoyin bada agaji dake cikin kasar na cigaba da kokawa da karancin kayayyakin da waɗannan mutane miliyan guda da rabi ke nema.kamar yadda kakakin kungiyar Agaji ta Red cross Joe Lewry yayi bayani...

"Kawo yanzu dai a kalla mutane dubu 20 ne kachal muka iya isa garesu da tallafi,matsalar da muke fama dashi shine,babu isassun kayayyakin .Amma da tallafi daga waje zamu iya fadada ayyukanmu"