Taron koli kan 'yan gudun hijira a Jamus
September 25, 2015Muhimman batutuwa na sakamakon taron kolin kan 'yan gudun hijira da ya gudana a fadar shugabar gwamnati da ke birnin Berlin, tsakanin gwamnatin tarayyar Jamus da gwamnatoci 16 na jihohin kasar sun hada da batun daukar nauyin 'yan gudun hijira, wanda kawo yawo yanzu akasari kananan hukumomin kasar ne ke samar da kudin wannan dawainiya. Yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayyar da jihohin ta nadai ba wa kowane mai neman mafaka Euro 670 a duk wata, kamar yadda shugabar gwamnati Angela Merkel ke cewa:
Euro 670 ga masu neman mafaka
"Gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar daukar nauyin ba da Euro 670 kowane wata ga duk mai neman mafakar siyasa, farawa daga ranar da aka yi masa rajista karkashin tsarin duba takardunsa har zuwa lokacin da za a kammala duba bukatun da ya gabatar. Za mu kuma ba da gudunmawa wajen aikin samar da gidaje da kudinsu ya kai Euro miliyan 500 da kuma shirin tallafa wa yaran da ke shigowa su kadai da zai ci Euro miliyan 350 a shekara."
A jimlance kudaden tallafin da gwamnatin tarayya za ta ba wa jihohi da kuma kananan hukumomi a wannan shekara sun kai Euro miliyan dudu biyu sannan a shekarar 2016 za su ta-samma Euro miliyan dubu hudu.
Taron ya kuma ayyana kasashe uku na yankin Balkan da suka hada da Albaniya da Kosovo da kuma Montenegro a matsayin kasashen da ke da kwanciyar hankali da lumana a wani mataki na rage yawan 'yan kasashen da ke shigowa Jamus don neman mafakar siyasa. Da yawa daga cikin shugabannin Jamus na masu ra'ayin cewa dalilan matsin tattalin arziki ke sa 'yan yankin na Balkan shigowa Jamus.
Matsin tattalin arziki na taka rawa
"Mun kuma amince da wasu kasashe a matsayin 'yan tudun mun tsira. Sannan mun jaddada cewa za mu kirkiro da sababbin guraben aikin sa kai dubu 10 na yi wa kasa hidima, inda za mu ba wa masu neman mafakar siyasa kakkyawar damar cancantar zama cikin kasa."
Firimiyan jihar Brandenburg wanda kuma shi ne shugaban babban taron gwamnonin jihohin tarayya, Dietmar Woidke ya nuna farin cikinsa ga sakamakon taron ina ya ce:
"A gani na a wannan rana mun amince da jerin matakai a wannan yarjejeniya da suka zama wajibi bisa la'akari da kalubalen da ke gabanmu. Wannan kuma wani sako ne gare mu baki daya cewa sai mun hada kai sannan za mu iya fuskantar wannan kalubale."
Sauran takwarorinsa na jihohin Tarayyar Jamus sun yi maraba da sakamakon taron da suka ce yana zaman wani tabbaci ga kasafin kudinsu. Alkaluman da gwamnatin Jamus ta bayar sun nuna cewa a wannan shekara 'yan gudun hijira kimanin dubu 520 suka shigo kasar kana tana sa ran yawan 'yan gudun hijirar zai kai dubu 800 a wannan shekara.