Tallafin gina azuzuwa a makarantun karkara a Najeriya
August 31, 2016Alhaji Salisu Mamman wani mai Tallafa ma Al’umma a jihar Katsina ya gina wata makaranta mai azuzuwa 17 a kauyen Kadandani da ke karamar hukumar Rimi a jihar Katsina da nufin tallafama yaran wannan yanki su ma su samu ingantaccen ilmin boko. Yanzu haka dai wannan makaranta ta kama aiki gadan-gadan wajen koyar da yaran karatu.
" Ni malamin makaranta ne kusan shekara 19, dan haka na san mahimmancin ilimi a zamantakewar dan Adam. Kuma babu wani abin da za ka yi wa al'umma a matsayin gudunmawa da wuce ka taimaka masu musamman 'ya'yansu su samu ilimi, musamman mu da muka fito daga yankunan karkara"
Mamman ya ce wannan makaranta an dade da kirkirarta amma ba'a samar mata da azuzuwaba sai dai tsugunne yaran suke hakan ne ya sa ya yi kokarin tallafa masu:
" Shekaru takwas da suka gabata ne muka kafa wannan makaranta, kuma muna gudanar da ita. NI na dauki dawainiyar kusan rabbin kudin malaman makarantar nan yau shekara tara, kuma ban fasa ba"
Suma iyayen daliban dama daliban da kansu da aka yi wannan makaranta domin su, sun bayyana gamsuwarsu da ita. Ilimi dai na daya daga cikin abunda ka iya maida dan talaka zuwa kololuwar mukami sannan tallafama al,umma wani abu ne wanda ke nusar da sauran al,umma suma su bada gudummuwarsu