1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD na neman tallafa wa siriya da kusan dala miliyan 400

February 15, 2023

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, a yayin kaddamar da neman taimakon a Amirka a ranar Talata, ya ce matakin zai samar wa mutum kusan miliyan biyar tallafi na tsawon watanni uku a Syria.

https://p.dw.com/p/4NUXp
Hoto: Syrian Presidency/Facebook/AP Photo/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da asusun neman tallafin kudi Dala miliyan 397 domin tallafa wa mutanen da girgizar kasa ta shafa a kasar Syria, inda lamarin ya yi munin da dubban mutane suka mutu, miliyoyi kuma ke cikin matsananciyar bukatar agaji.

Majalisar Dinkin Duniyar ta neman tallafin ya zama wajibi ganin yadda mako guda bayan girgizar kasar , miliyoyin mutane ke ci gaba da tagayyara, inda wasunsu suka rasa gidaje ba tare da kayan dumama jikinsu ba duk da yanayin hunturu da ake ciki.

To sai dai kuma Guterres ya yi kira ga hukumomin Syria da su bude kofofi ga masu bayar da kayan agaji yadda taimako zai isa ga mutanen da ke da bukata. Syria wacce kafin girgizar kasar ta kwashe shekaru 12 a cikin yakin basasa, ta tsuke hanyoyin shigar da kayan agaji a kasar, inda ta bar hanya daya tilo da aka rika wannan aiki.