Tarayyar Turai ta gayyaci Trump taro
November 9, 2016A wata sanarawar taya murna da suka rubutawa Trump sun ce suna gayyatarsa zuwa nahiyar Turai, sun kuma nunar da cewa a shirye suke su tattauna da shi dangane da batun sauyin yanayi da yaki da ta'addanci da kuma rikicin Ukraine. A nasa bangaren ministan harkokin kasashen ketare na Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bukaci da a gudanar da taron ministocin kasashen ketare na Tarayyar ta Turai a ranar Lahadi mai zuwa. Shi kuwa shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya nunar da cewa Amirkawa sun zaba wa kansu abin da suke so:
"Amirkawa sun magantu. Sun zabi Donald Trump a matsayin shugaban kasarsu. Ina tya shi murna kamar yadda yake a bayyane tsakanin shugabannin kasashen da ke gudanar da mulkin dimokaradiyya. Na tsammaci Hillary Clinton za ta samu nasara kasancewar na yi aiki tare da ita. Zaben Amirka ya bude babi na rashin tabbas. Abu ne da zan so in tunkare shi da nutsuwa."