1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lebanin za ta samu tallafin kudi

Suleiman Babayo MAB
May 2, 2024

Kasar Leban za ta samun tallafin makuden kudi daga Hukumar Tarayyar Turai kan yaki da bakin haure masu neman shiga kasashen Turai da hanyoyin da suka saba ka'ida.

https://p.dw.com/p/4fQwg
Shugabar hukumar ta Tarayyar Turai Ursula von der Leyen
Shugabar hukumar ta Tarayyar Turai Ursula von der LeyenHoto: Mohamed Azakir/REUTERS

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi alkawarin ba da taimakon kudi kimanin Euro milyan dubu ga kasar Lebanon domin tayar da komadan tattalin arziki gami da dakile bakin haure masu neman zuwa kasashe Turai musamman 'yan gudun hijira daga kasar Siriya, da yanzu haka suke rayuwa a kasar ta Lebanon.

Shugabar hukumar ta Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta bayyana haka a wannan Alhamis a birnin Beirut fadar gwamnatin kasar ta Lebanon inda take ziyarar aiki. Lokacin ziyarar von der Leyen ta gana da Firaminista Najib Mikati na Lebanon inda ta nuna aniyar kasashen kungiyar Tarayyar Turai na taimakon hukumomin tsaron Lebanon da horo gami da kayan aiki domin iya kare iyakokin kasar.