Tarihin Idi Amin Dada
October 21, 2010Idi Ami an haishe a garin Aruwa na ƙasar Uganda, amma babu wanda ya san shekara da aka aihe shi.Saidai an tabbatar da cewa ya zo duniya tsakanin 1923 zuwa 1928. Kuma a lokacin da ya ke raye bai fidda mutane jahilci ba game da shekara aihuwarsa.
Abinda aka sani dai shine ubansa Andreas Nyabire soja ne a rundunar sojojin ƙasar Sudan zamanin turawan mulkin mallaka, daga cen ne ma ya tuba zuwa addinin musulunci, aka rada masa suna Amin.Ya rasu a shekara 1976 wato shekaru 34 kenan.
Sanan ma´aifiyarsa sunanta Assa Atte kuma ta yi suna matuƙa wajen maita.Shekaru kaɗan bayan aihuwar Idi, iyayensa su ka rabu.Saboda haka wajen uwarsa ya girma.
A shekara 1946 ya shiga soja, mutum ne ƙaƙƙarfa ga shi da tsawo ga kuma jiki. Tun da wuri sojojin mukin mallaka su ka lura da ƙoƙarinsa da kuma rashin imaninsa a duk lokacin da aka tura tawagar soja kwantar da wata tarzoma.Daga shekara 1951 har zuwa 1960 Idi ke riƙe da matsayin zakaran wasan dambe na ƙasar Uganda.
Saboda jarumtakar da ya ke nunawa a aikin soja ya sa turawa su ka bashi matsayin Litana a shekara 1961.
Sai kuma shekara ta gaba wato 1962 Uganda ta samu ´yancin kanta.A lokacin nan ya samu ƙarin girma daga Litanan ya hau zuwa Janar bugu da ƙari turawan Birtaniya su ka naɗa shi mataimakin shuganan rundunar soja ta ƙasar Uganda.
Sai kuma a shekara 1966 Firayim Ministan Yuganda Milton Obote ya naɗa Idi a matsayin shugaban rundunar sojoji.
A lokacin da aka naɗa Idi Amin Dada a matsayin shugaban rundunar sojoji ta ƙasa,ya yi amfani da wannan dama domin ƙara samun gidin zama ta hanyar cusa kuratan sojojin ´yan ƙabilarasa cikin bataliyoyin soja, sannan ya ƙulla ma´amila da manya-mayan soja na ƙasashen duniya, mussamman na Birtaniya, wadda itace a lokacin take ɗaure masa gidin.
Sannu a hankali sai aka fara samun rashin jituwa, tsakanin Firayim Minista Obote da Idi Amin Dada, inda shi Firayim Ministan ya fara zargin Idi da shirya masa juyin mulki.
Da Idi ya gano cewar babu makawa Milton Obote sauke shi za shi daga muƙamin shugaban rundunar sojoji ta ƙasa, sai ya ce to bari ka gani, kamin ka sauke ni in sauke ka.Ta haka ne babu zato babu tammaha a shekara 1971,Idi Amin Dada ya shiryawa Firayim Ministan juyin mulki a lokacin da ya ke halartar taron ƙasashe masu amfani da halshenTuranci wato Commonwealth a Singapour.Saboda ɗaurin gindin da ya samu daga Birtaniya ba da wata wata ba, ƙasashen duniya su ka yi na´am da wannan juyin mulki kuma Idi ya samu karɓuwa.Cilas Firayim Ministan da aka hamɓare ya shiga gudun hijira a ƙasar Tanzaniya.Saboda ɗaurin gindin da ya samu daga Birtaniya ba da wata wata ba, ƙasashen duniya su ka yi na´am da wannan juyin mulki kuma Idi ya samu karɓuwa.
Kamar dai yadda rahotani su ka bayyana, Idi Amin Dada ya shinfiɗa cikkaken mulkin kama karya.Wasu rahotanin ma sun ce mutanen da ya sa aka kashe a tsawan mulkinsa za su kai kimanin mutane dubu ɗari biyar.Misali akwai lokacin da hamɓɓararen Firayim Ministan ya yi yunƙurin kifar da shi tun daga Tanzaniya tare da taimakon sojojin Tanzaniya da kuma na Yuganda da su ka shiga gudun hijira.Da ya fusata sai Idi sai ya sa aka hallaka duk manya sojoji na ƙabilar Acholo da Lango, sannan kuma ya ƙaddamar da wano gagaramin hari ga ƙasar Tanzaniya.
Bayan haka ta fannin tattalin arziki shekara ɗaya bayan hawansa karagar mulki ya kori ´yan kasuwa 70.000 ´yan asulin Pakistan, Indiya da yahudawa,wanda a lokacin su ne ke mamaye da harakokin kasuwancin Uganda.
Wannan mataki ya haddasa taɓarɓarewar hada-hadar kasuwancin matuƙa, to amma kuma wasu na kalon shi a matsayin wani mataki na nuna kishin ƙasa.
Daga cikin aiyukan da yi Idi Amin Dada ya riƙe muƙamin shugaban Ƙungiyar Ƙasashen Afrika ta OAU a shekara 1975.
Hausawa ke cewa wai ba farau ba ke da ciwo ramau,yadda ya samu mukami ta anyar juyin mulki ta wannan hanya ce shima ya sauka.
A ƙasar Tanzaniya inda Firayim minista Milton Bobote ke gudun hijira, ya girka wata ƙungiyar soja wadda ya raɗawa suna NFOL wato Ƙungiyar ƙwato yancin ƙasar Uganda,wadda ta ƙunshi manyan sojojin Yuganda da ke gudun hijira, wannan Ƙungiyar tawaye ta samu goyan bayan ga gwamnatin Tanzaniya.
A watan Oktoba na shekara 1978 lokacin da Idi Amin Dada ya sake kai hari ga ƙasar Tanzaniya, sai aka gama ƙarfi tsakanin ƙungiyar tawayen da sojojin Tanzaniya, wasu na cewa ma tare da taimakon Israela.
A wannan hari sun yi nasara ƙwatar mulki a watan Janairun 1979.
Kamin su samu su cafke shi sai Idi Amin Dada ya ranta cikin na kare tare da matansa huɗu da ´ya´yansa.Da farko ya yada zango a Libiya, daga nan kuma ya cigaba zuwa Saudi Arabiya inda ya samu mafakar siyasa.Gwamnatin Saudi Arabiya ta bashi gida , tare da ɗaukar yauninsa gaba ɗaya da iyalinsa a matsayin godiya ga ƙoƙarin da yayi wajen ɗaukaka addinin Islama.
Idi Amin Dada ya rasu a birnin Djidda na ƙasa mai tsarki ranar 16 ga watan Ogusta na shekara 2003.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Ahmad Tijani Lawal