Tarihin marigayi Mano Dayak madugun 'yan tawayen abzinawan Nijar
December 24, 2012Mano Dayak ya rubuta littatafai da dama, a cikin ɗaya daga wannan littatafi mai suna "Touareg, la Tragedie" ya yi tarihin kansa da kansa. Ya ce an haihe shi wajejen farkon damanar shekara 1950, wato yanzu 62 kenan da suka gabata a wata ruggar abzinawa dake Tidene, mai tazar kilomita 100 a arewacin Adagez.Ya ce ma'aifinsa makiyayin rakuma ne sannan kuma mahaifiyarsa ta na kiwan awaki.Kamin ya shiga makaranta bai san ko ina ba,illa wannan rugga ta Tidene.
A wurin iyayensa ya laƙanci yankin Air gaba ɗaya, da kuma ƙabli da ba'adin al'adun abzin.
Mano Dayak ya yi karatun firamare a wata makarantar makiya, a garin Azzel.Bayan ya kamalla sakandare matakin farko a shekara 1970 a Agadez,ya ci gaba da karatu a ƙasar Amirika,inda ya samu Baccalaureat sannan, kuma ya fara karatun jamai'a.Bayan nan ya tafi ƙasar Faransa, inda yayi karatu ta fannin tarihin ƙabilu a wata mai karanta mais una Ecoles Pratiques des Hautes Etudes, sannan ya yi karatu a ƙasar Faransa.
Lokacin da ya dawo gida Nijar yayi zama dan jagorar turawa masu yawan shkatawa a jihar Agadez,kamin daga bisani ya girka wani kamfani mai kula da yawan shakatawa mai suna Temet Voyages.
Lokacin da ya na ƙasar Faransa ya nuna shawar shiga wasan tsere motocin nan da aka fi sani da suna Rally Paris-Dakar.An dama da shi cikin wannan tsere daga 1986 zuwa 1988.
Mano Dayak na daga mutanen da suka ƙirƙiro tawayen abzinawa a Jamhuriya Nijar.
Idan mu ka dan koma cikin tarihi, a shekara 1973 an yi wata mumunar yinwa a Nijar,inda abzinawa da yawa su ka ƙaura zuwa Libiya, gwamnatin Khaddafi ta karɓe su kuma baiyanai sun nuna cewar daga nan ne aka fara kitsa tawayen abzinawa a Jamhuriya Nijar. Lokacin da mariganyi shugaba Ali Chaibou ya hau karagar mulkin Jamhuruiya Nijar, bayan mutuwar Janar Seini Kountche,ya ƙaddamar da wani tsari wanda aka raɗawa suna "Decrispation", wato ba al'umar ƙasa 'yancin walwala da 'yancin faɗin albarkacin baki, bayan mulkin kama kariya na tsawan shekaru 14.A ƙarƙashin wannan tsari ne, Ali Chaibou yayi kira ga duk 'yan Nijar dake zaune a ketare su dawo gida domin su bada haɗin kai ayi aikin ƙasa, saboda haka kusan abizinawa dubu 20, su ka dawo gada Aljeriya da Libiya.
Akwai lokacin inda abzinawa su ka yi fito na fito da dakarun gwamnatin Nijar a cikin yankinTchintabaraden na jihar Tahoua, daga wanan lokace al'amuran suka rinacabe, kuma daga nan ne Mano Dayak ya ƙirƙiro ƙungiyar tawayen abzinawa mai suna FLT wato Front de Liberation du Tamous, dakarun kwatar 'yancin Tamous wani yanki ne a jihar ta Agadez.Mano Dayak ya ƙirƙiro wannan ƙungiyar tawaye a shekara 1993, bayan wannan ƙungiya gungun abizinawa daban-daban sun yi ƙirƙiro ƙungiyoyin tawaye iri-iri.Saboda gama ƙarfi wuri guda, sai Mano Dayak tare da sauran shugabanin ƙungiyoyin tawaye su ka girka haɗɗaɗiyar ƙungiyar tawayen abzinawa da suka raɗawa suna CRA wato Coordination de la Resistance Armée.
Rasuwar Mano Dayak:
Ranar 15 ga watan Desemba na shekara 1995, a wannan ranan ce ta kamata Mano Dayak tare da wasu shugabanin tawaye biyu su gana da shugaban ƙasar Nijar Mahaman Usman game da batun zaman lafiya.Sun shiga jirgi daga Agadez zuwa Yamai, jim kaɗan bayan tashin jirgin yayi salla da ka ya fadi, saboda a cikin wannan haɗari ne Mano Dayak ya rasu, ranar 15 ga watan Desemba na shekara 1995 wato yanzu shekaru 17 kenan.
Saboda karramma Mano Dayak ne tsofan shugaban ƙasar Nijar marigayi Janar Ibrahim Baare Mainasara, ya radawa suna filin saukar jiragen sma na Agadez sunan Mano Dayak.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman