Tarihin shugaban Siriya Bashar al-Assad
September 30, 2013Bayan kammala karatunsa na frimary da College da kuma Sakandry Bashar ya shiga jami'a a birnin Damascus a shekarun 1982 inda ya karanta aikin likitan ido, wanda kuma a shekarun 1988 ya samu digiri a wannan fannin.
A ci gaba da karatunsa domin neman ƙorewa a kan aikin na likitan ido Bashar Al Assad ya tafi ƙasar Ingila a shekarun 1992 a birnin London.
Karatun da Bashar-al-Assad a cikin manyan jami'oi
A jarrabawa ta farko da ya yi domin fara kwas a wani asibitin na Saint Mary Hospital Werster Eye Hospital Assad ya gaza samu nasara sai a zagaye na biyu ya samu a lokacin ne kuma ya fara aiki a ƙarƙashin dokto Schulu Lenberd da ke a Marys Hospital. A can ne Bashar ya sadu da matarsa wadda ya aura Asma Al Aklhas yar Ingila mai asilin Siriya yar ɗarikar sunni da ke aiki a bankin City JP Morgan.
Shigar Bashar-al-Assad cikin harkokin siyasa
Bashar-al-Assad ba a yi tsamani zai sami mulkin na Siriya ba domin tun can da farko mahaifinsa Hafez El Assad ya shirya babban ɗansa na farko Bassel ya gaje shi a kan mulkin to sai dai a shekarun 1994 rai ya yi halinsa Bassel ya mutu a cikin wani hatsarin mota. Abin da ya sa Hafez -el Assad ya yi kira ga ƙaramin ɗansa Bashar da ya gaje shi inda ta Allah ta zo. A lokacin ne Bashar ya dawo daga Ingila ya shiga makarantar koyon aikin soji,a lokaci kaɗan ya sami muƙamin kanal kuma lokacin da maihafinsa ya mutu yana da shekaru 34. A wannan lokaci dai dokar ƙasar ta Siriya ta ce tsayawa takarar shugaban ƙasa sai mai shekaru 40, amma take-yanke majalisar dokokin ƙasar ta dawo da addadin zuwa shekaru 34.
Abin da ya ba da dama aka naɗa Bashar Al Assad a matsayin shugaban ƙasa a ranar 25 ga watan Yuni na shekara ta 2000 kafin a ranar 10 ga watan Yuli na shekara ta 2000 a yi ƙuri'a raba gardama inda al'ummar Siriya ta amince da shi matsayin na shugaba.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe