1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanni na nazari kan illolin sauyin yanayi a Masar

Zainab Mohammed Abubakar M. Ahiwa
November 7, 2022

Shugabannin kasashen duniya masu yawa ne ke halartar taron sauyin yanayi da ke gudana a sanannen wurin shakatawan nan na Sharm el-Sheikh da ke a kasar Masar.

https://p.dw.com/p/4J8Zn
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Shugabanin kasashen duniya sama da 100 ne ke halartar taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya da aka yi wa lakabi da COP27, a wurin shakatawa na Sharm el-Sheikh da ke a kasar Masar. Taron da aka soma a wannan Litinin, za a kwashe tsawon makonni biyu ana yi, kuma zai duba sabbin matakan da suka kamata a dauka domin shawo kan matsalolin da sauyin yanayin ke haifar wa rayuwar dan Adam da muhallinsa.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonia Guterres ya gargadi shugabanni da ke halartar taron kan sauyin yanayi cewar, duniya na cikin tsaka mai wuya da ke bukatar daukar matakan gaggawa na taron dangi kan matsalar dumamar yanayi. 

A cewarsa manyan kasashe biyu da suka karfin tattalin arziki, watau Amurka da China suna da alhaki na musamman wajen hada karfi da karfe don tabbatar da nasarar wannan yarjejeniya a aikace, kuma wannan shi ne fata daya da ake da shi na cimma manufofi kan yanayi. Mutane na da zabin ko a hada kai a warware matsalar sauyin yanayi ko kuma a taru a yi kunar bakin wake.

Antonio Guterres a taron COP27
Hoto: Gehad Hamdy/dpa/picture alliance

Sai dai shugaba Xi Jinping na China wanda kasarsa ce ta fi kowace fitar da hayaki mai guba a duniya, ba ya cikin mahalarta taron na COP27. A yayin Joe Biden na Amurka da kasarsa ke zama ta biyu a wannan ta'asar ana sa ran zai hade a taron na COP27 wani lokaci nan gaba, bayan gudanar da zaben tsakiyar wa'adi a ranar Talata, inda ake kyautata zaton 'yan jam'iyyar Republican da ke adawa matakan sauyin yanayin za su karbi shugabancin majalisa. 

Shugabannin kasashe masu tasowa sun yi farin cikin jin cewar mahalarta za su bukaci kudaden diyya cikin ajandar taron saboda asarar da aka tafka. Kamar yadda mai fafutuka daga gabashin Afirka Evelyn Acham ta nunar. Ta ce mutane a nahiyar Afirka dai suna shan wahalar bala'o'in da ke faruwa, kama daga ambaliyar ruwa a Najeriya zuwa wasu bala'o'i, ya kamata shugabannin duniya su ba da wadannan misalan a tattaunwar taron na COP27 domin tunkarar wadannan matsaloli.

Amurka da kasashen Turai dai sun dauki shekaru masu yawa suna jan kafa wajen aiwatar da wannan yarjejeniya. Sai dai a wannan karon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce wajibi ne a tsayar da wa'adin bayar da kudaden diyya na irin wadannan asara da wahalhalu da aka fuskanta. Kuma shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Mohammed bin Zayed Al-Nahyan na cikin wadanda suka yi maraba da hakan.