1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Nemo mafita kan tsaro

Lawan Boukar LMJ
September 5, 2019

An gudanar da wani taro na 'yan jaridu a Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar, da ya hadar da 'yan jaridu da masana kan harkar tsaro na kasashen yankin Sahel.

https://p.dw.com/p/3P5cw
Nigeria Soldaten in Diffa
Nijar na daga cikin kasashen yankin Sahel da ke fuskantar matsalar rashin tsaroHoto: Reuters/J. Penney

Taron wanda gidauniyar Konrad Adenauer ta Jamus ta shirya, ya tabo batutuwa da dama kan rawar da 'yan jarida za su iya takawa wajen wallafa labarai kan harkar tsaro da ta'adanci. Mahalarta taron dai sun tattauna kan batutuwa masu yawa da suka hadar da hatsarin da 'yan jaridar ke fuskanta wajen wallafa labaran harkar tsaro da, kuma yadda za a shawo kan matsalar. Taron dai ya nunar da cewa akwai bukatar a bai wa 'yan jaridun da suka hadu daga kasashe dabam-dabam wani horo da zai taimaka musuwajen udanar da ayyukansu kana a hada hannu waje guda domin samo musu mafita.  A hannu guda kuma, 'yan jaridun da suka samu halartara wannan taro sun nuna jin dadinsu tare da bayyana cewa sun fahimci matsalolin da suke fuskanta kuma hakan na zaman mataki na farko wajen shawo kan tarin matsalolin da suke fuskanta.