Taron bada agaji ga kasar Siriya
January 15, 2014Taron da kasar Kuwait ta karbi bakuncinsa dai shi ne taro na neman agaji mafi girma a tarihi, kuma kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce matsanancin halin da aka shiga a kasar ne ya tilastawa kasashen duniya da Majalisar Dinkin Duniya yanke shawarwar shirya taron don neman wannan tallafi.
Tuni dai wakilan kasashen duniya ciki har da na Amurka waddda ke kan gaba wajen tallafawa kasar ta Siriya da kuma hukumomin bada agaji na duniya suka isa Kuwait din tun a jiya Talata don gudanar da wannan taro, inda a hannu guda shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da aniyarsa ta kara agaji na cimaka da ya ke bawa wadanda ke cikin hali na bukata a Siriyan.
Rikicin na Siriya dai ya zuwa yanzu ya hallaka mutane sama da dubu 130 wanda galibinsu fararren hula.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu