1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TARON BANKIN DUNIYA DA IMF DA RUKUNIN G - 7 A BIRNIN WASHINGTON.

YAHAYA AHMEDApril 18, 2005

Ministocin kudi na kasashen rukunin nan na G-7, mafi arzikin masana'antu a duniya, sun halarci wani taron da asusun ba da lamuni na duniya, wato IMF da bankin duniya suka shirya a birnin Washington don tattauna batun komadar tattalin arzikin kasashen duniya da kuma hauhawar farashin man fetur da ake ta fama da shi a halin yanzu.

https://p.dw.com/p/BwUi
Hans Eichel, ministan kudi na tarayyar Jamus.
Hans Eichel, ministan kudi na tarayyar Jamus.Hoto: AP

A taron da suka yi a birnin Washington a ran asabar da ta wuce, ministocin kasashe masu ci gaban masana’antu na rukunin nan da aka fi sani da suna G-7, sun yi dari-dari da wasu alkaluman da Asusun ba da Lamuni na Duniya, wato IMF, ya buga, wadanda ke hasashen bunkasar tattalin arzikin kasashen duniya a cikin wannan shekarar da kuma shekarar badi. Dalilin nuna shakku da ministocin ke yi kuwa, shi ne kasadar da hauhawar farashin man fetur a kasuwannin duniya ke janyowa. Ministan kudi na tarayyar Jamus, Hans Eichel, wanda shi ma ya halarci taron, ya bayyana cewa:-

"Mun dai yi tattaunawa mai zurfi game da wannan matsalar ta hauhawar farashin mai. Wannan matsalar dai ita ce babbar kasada ga bunkasar tattalin arziki a halin yanzu. Farashin dai sai kara habaka yake yi. Ba za a iya kuma yin hashensa ba. Hakan ne kuwa ke janyo mana damuwa. Amma duk da haka, a yanzu, dogarar bunkasar tattalin arziki kan farashin man fetur, ta ragu, idan aka kwatanta ta da da."

Haka dai lamarin yake a nan Jamus. Idan aka dubi shekaru 30 da suka wuce, za a ga cewa, yawan makamashin da kasar ke samowa daga man fetur ya ragu daga kashi 50 cikin dari zuwa kashi 37 cikin dari. Kazalika kuma, an sami ragowa ainun, na kudaden da masana’antun Jamus ke kashewa kan man fetur a cikin wadannan shekarun. Idan ko aka waiwaya zuwa yankin Asiya, sai a ga cewa, yawan makamashin da Sin da Indiya ke bukata, ya ninka na Jamus har sau 8. Yankin Asiyan da kuma Amirka ne dai, ake yi musu kallon jagoran bunkasar tattalin arzikin duniya, yayin da shacin nan mai amfani da kudin Euro, musamman ma dai Jamus, ke can baya-baya. Amma, bunkasar tatttalin arziki a Amirkan, tana tafe kuma da wata kasada, wato ta habakar basussukan da kasar ke ta ciyowa. A halin yanzu dai basussukan Amirkan sun kai kimanin dola biliyan 60. Ministocin kudin kasashen rukunin G-7 din dai sun nuna matukar damuwarsu ga gibin kasafin kudin da ake ta kara samu a Amirkan. A ganin Hans Eichel dai:-

"A lokaci mai tsawo, ba za a iya ci gaba da cike gibin kasafin kudin Amirka da manyan bankunan kasashen Asiya suka yi ta yi a shekarun baya ba. Kamata ya yi dai a kago wasu dabaru da za a iya dogaro da su a matsakaicin lokaci. Duk da hakan ma, dabarun ba za su takaita darajar kudade ne kawai ba. Kafin a cim ma nasara, sai Amirka ta yunkuri daukan karin matakan tsimi don rage gibin kasafin kudinta."

Ministocin kasashen rukunin G-7 da jami’an IMF din dai, sun kasa cim ma daidaito kan samad da kudade don ba da taimakon raya kasashe. An dai lura da cewa, a cikin shekaru 10 da suka wuce, yawan kasafin kudin ba da taimakon raya kasashe daga gamayyar kassa da kasa, ya ragu matuka. Sabilin da hakan ne kuwa, wasu masu sukan lamiri ke ganin cewa, idan dai ba a kara yawan kasafin kudin da ake warewa don ba da taimakon raya kasashe ba, to gurin nan da aka sanya a gaba, na rage yawan talauci a duniya zuwa rabin adadinsa na shekara ta 2000, kafin shekara ta 2025, zai kasance ne kamar wata almara.

Ra’ayoyin Amirka da na Turai dai sun bambanta a kan wannan batun. Yayin da Amirkan ke tunanin daukan matakan soke wa wasu kasashe matalautan basussukansu, nahiyar Turai na yunkuri ne na kago wasu sabbin hanyoyin samad da isassun kudade don bunkasa manufar, ta ba da taimakon raya kasashe. Ta yin la’akari da matsalolin gibin kasafin kudin da suke huskanta a tattalin arzikinsu, kasashen Turan sun fi gwammacewa ne da daukan sabbin mattakai na sanya haraji kan masana’antun sufuri. A lal misali, Faransa da Jamus sun ba da shawarar sanya haraji kan hada-hadar sufurin jiragen sama. Kamar dai yadda Hans Eichel ya bayyanar:-

"Idan muka dauki alal misali man da jiragen sama ke sha. Jiragen sama da dama ne ke tashi daga nan Jamus. Abin da ke nuna cewa, Jamusawa ma za su ba da gudummuwarsu a wannan yunkurin. A nan dai babu wanda za a kwara. Amma muna bukatar wasu ka’idoji kafin mu iya iawatad da wannan shirin. Idan ko ba haka ba, kasafin kudinmu kawai ba zai iya daukar wannan nauyin ba. Kuma ba Jamsu kawai ne wannan lamarin ya shafa ba."

A wannan shekarar ma, masu adawa da salon nan na hadayyar tattalin arzikin duniya, ko kuma Globalisation a turance, sun yi zanga-zanga a birnin na Washington a lokacin taron, inda suka zargi kafofin kudin na kasa da kasa, da tafiyad da manufofin siyasar rashin nuna adalci ga kasashe masu tasowa.