Taron shugabannni uku
May 8, 2018Talla
Firaminista Li Keqiang na China ya fara ziyarar aikin kwanaki hudu a kasar Japan, kuma babban jami'in na farko da ke irirn wannan ziyarar cikin shekaru bakwai. Lokacin ziyarar zai halarci taron da shugabannin kasashen Japan da kuma Koriya ta Kudu game da halin da ake ciki a mashigin ruwan Koriya, kan batun nukiliyar Koriya ta Arewa.
Sannan Firaminista Li Keqiang na China zai tattauna da Firaminista Shinzo Abe na Japan da Shugaba Moon Jae-in. Shi dai Shugaba Moon Jae-in ke zama shugaban Koriya ta Kudu na farko da zai ziyarci Japan cikin shekaru shida da suka gabata.