Taron G20: AU na dakon goron gayyata
September 6, 2023A makonnin baya firaministan Indiya Narendra Modi ya mika wa kungiyar AU tayin zama mamba na din-din-din a kungiyar ta G20 wacce ke samar da kashi 85 cikin dari na arzikin duniya.
Karin bayani: Taron G20 ya karkata ga kasuwanci da tsaro
To sai dai a wata hira da manema labarai, mai magana da yawun kungiyar Ebba Kalondo ta ce yayin da ya rage kwanaki uku kacal a buda taron na birnin New Delhi har kawo yanzu AU ba sami goron gayyata a hukumance ba.
Karin bayani: An kasa cimma matsaya a taron G20
Kugiyar tarayyar Afrika dai mai ofishi a birnin Adis Ababa na kasar Habasha ta kunshi kasashe 55 wadanda ke samar da albarkatu da kudinsu ya haura biliyan 3.000 na dalar Amurka. Wannan ne ma ya sa a can baya shugaba Joe Biden na Amurka ya bayyana fatan sama wa Tarayyar Afrika gurbi a kungiyar ta G20 yana mai cewa abu ne da zai iya kara masu karfi.