1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron gaggawa na ministocin kiwon lafiya na tarayyar Turai a London

October 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvOc

Ministocin kiwon lafiya na kasashen KTT sun hallara a birnin London na kasar Birtaniya inda tattauna akan matakan da za´a dauka wajen dakile yaduwar cutar ta murar tsuntsaye. Bayan bullar nau´in kwayoyin cutar mai hadari ga dan Adam a kasashen Romaniya da Turkiya, ake yi ta fargabar cewar cutar ka iya shigowa kasashen tarayyar Turai nan ba da dadewa ba. Da farko kasashe 25 membobin kungiyar ta EU sun ce suna shirin haramta sayo kaji da tsunsaye daga Rasha bayan bullar murar tsuntsayen a kudu da birnin Mosko. Wannan taron gaggawa ya zo ne bayan wani gwaji da aka gudanar a Girika bai tabbatar da bullar cutar a can ba, ko da ya ke har yanzu ana jiran sakamakon karshe na wannan gwaji.