1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron IMF da Bankin duniya

October 8, 2010

IMF tare da Bankin duniya, suna gudanar da babban taron su a birnin Washington na kasar Amirka, domin tattauna batutuwan da suka shafi kudi a duniya.

https://p.dw.com/p/PZq3

Shugabannin sassan da ke kula da harkokin kudi a kasashen duniya daban daban, sun hallara a birnin Washington na kasar Amirka ne a kokarin da suke yi na shawo kan cece - kucen da manyan kasashen duniya musamman Amirka ke yi game da bukatar daga darajar takardar kudin China ta yadda hakan zai dace da bukatun manyan kasashen.

A lokacin taron na wannan Jumma'ar, sakataren kula da baitul - Malin Amirka Timothy Geithner ya bukaci asusun bayar da lamuni a duniya na IMF daya dauki matakan warware matsalar da ta taso akan batun darajar kudin, duk da cewar ya na da ra'ayin cewar, akwai bukatar dukkan kasashen duniya su sauke nauyin da ke kansu.

Dominique Strauss-Kahn / IWF / Washington
Hoto: AP

Tuni dai dama Darektan Asusun na IMF Dominique Srauss-Kahn ya bayyana cewar, takaddamar fa tana da asali:

"Mutane da dama na yin amfani da kalmar nan ta yaki akan takardar kudi, nima ina jin ina yin anfani da ita ko da shike kamar ta yi tsauri sosai. Sai dai gaskiyar maganar ita ce wasu na daukar takardar kudin su a matsayin makamin yaki ne, wanda kuma ba zai yi alfanu ga tattalin arzikin duniya ba. Abinda muke bukata shi ne sake daidaita tattalin arzikin duniya, wanda kuma zai kasance yana da nashi ta'asiri ta fuskar kimar takardar kudi. Saboda haka yin adawa da wannan matakin, ba zai taimakawa shirin samar da daidaiton ba."

Takadama akan batun darajar kudin Chinan,ta yi kamari ne a dai dai lokacin da kasashen duniya daban dabanm ke kokarin farfadowa daga matsalolin tattalin arzikin da suka fada a ciki, wanda kuma ya sa kwararru ke cewar hakan zai kara yin tafiyar hawainiya wajen farfadowar tattalin arzikin duniya.

Akan hakane kuma shugaban babban bankin duniya, Robert Zoelick ya bayar da shawarar warware matsalar cikin ruwan sanyi:

" Muna cikin wadin rikicin tattalin arziki, wanda yasa ake tada jijiyoyin wuya. Shawara ta ita ce akwai bukatar bin sannu a hankali wajen shawo kan takaddamar da ta so domin gudun karuwar muninta. Idan ba haka aka yi ba, to, kuwa muna fuskantar hatsarin sake fadawa cikin rikicin tattalin arziki - makamancin na shekarun 1930."

Robert Zoellick / Weltbank / Washington
Hoto: AP

Kimanin ministocin kula da harkokin kudi da kuma shugabannin manyan bankuna daga kasashe 187 ne ke halartar taron na birnin Washington, wanda asusun bayar da lamuni a duniya na IMF tare da hadin gwiwar babban bankin duniya ke gudanar da shi - sau biyu a duk shekara.

Wani batun da taron ke tattaunawa kuwa shi ne kokarin da wasu kasashe ke yi na samun sukunin taka rawa wajen tafiyar da harkokin manyan cibiyoyin kudi a duniyar - ciki kuwa harda IMF, inda shugaban asusun Dominique Strauss-Kahn ya ce akwai fa abubuwan da za su biyo bayan wannan bukatar, wadanda kuma ya kamata a yi la'akari da su:

"Abinda na fahimta shi ne cewar, akwai kasashen da ke son a dama da su cikin tafiyar da sha'anin asusun bayar da lamuni a duniya na IMF, wanda ke tattare da nauyin irin abinda kasashen za su yi da kuma ta'asirin sa ga tattalin arzikin duniya."

A halin da ake ciki dai China ta yi watsi da bukatar daga darajar takardar kudin ta, wanda ta ce zai jefa sha'anin kasuwancin ta cikin hatsari, yayin da jami'ai daga Turai kuwa suka bayyana fargabar cewar, tashin martabar takardar Euro akan dalar Amirka da Yuan na China zai ci gaba da yin barazana ga farfadowar tattalin arzikin kasashen da kew yin amfani da Euro, inda Turai ta ce za ta yi matsin lamba a gare su su dauki matakin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu