Taron kare Muhali a Japan
October 30, 2010Ministocin kula da kare muhali da kuma yanayi na sama da ƙasashe 200 sun cimma wata yarjejeniya ta kare halitu da kuma tsirai dake fuskantar barazanar ɓacewa a doran Duniya.Ministocin wanda suka cimma wannan shiri a ƙarshen taron da aka kammala a jiya a birnin Nagoya na ƙasar Japan bayan makonnin biyu na tattaunawa, sun fitar da wata sanarwa mai shafi 20 da ta tanadi kare dazuzzuka da halitu, dakuma tsirai .
kafin nan da shekara ta 2020, tare kuma da tilasawa gwamnatocin ƙasashen kula da kiyaye ga shawarwarin da aka cimma.
Hubert Refuser Shugaban haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyin dake fafutakar kare muhalli na nan ƙasar Jamus ya shaida cewa wannan wata babbar nasara ce
Oton
wannan mahawara wani mataki ne na farko kafin a kai ga gaci domin zai kara bada himma a Duniya
na cewa mu duka alhaki ya rataya a wuyanmu na yin wanin yunkuri a cikin ƙasashe masu tasowa da kuma waɗanda ke da arzikin masana'antu akan wannan batu
Mawallafi:Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar