Taron kasashen duniya masu fada aji a London
January 16, 2006Manyan kasashen duniya biyar dake da cikakken iko a kwamitin sulhu na Mdd tare da Kasar Jamus na ci gaba da gudanar da taron kolin su a birnin London, don daukan matakin daya dace akan kasar Iran.
Kafin dai wannan taro na yau, kasashen Jamus da Faransa da Biritaniya sun bukaci shigowar Mdd cikin wannan al´amari don ladaftar da kasr ta Iran a makon daya gabata.
Daukar wannan mataki ya samo asaline bayan da mahukuntan na Iran suka bayar da sanarwar ci gaba da bincike a wasu tashohin nukiliyar su dake cikin kasar.
Ya zuwa yanzu dai kasashen yamman tare da Amurka sun zargi kasar ta Iran da kokarin kera makamin nukiliya, wanda kuma tuni kasar ta Iran ta karya hakan da cewa nukiliyar da take kokarin kerawa na bunkasa hasken wutar lantarki ne, amma bana tashin hankali ba.
Manyan kasashe biyar din dake halartar wannan taro na birnin London, sun hadar da Faransa da Biritaniya da Amurka da Russia da kasar Sin a hannu daya kuma da tarayyar Jamus