Muhammed Bande: Muhalli gimshikin taron MDD
September 23, 2019Manyan batutuwan da za su dauki hankali a babban taron koli na Majalisar Dinkin Duniya sun fi karkata kan batun canjin yanayi inda a cikin wata hira da ya yi da tashar DW shugaban zauren Majalisar Dinkin Duniya Farfesa Tijjani Muhammad Bande shi ya bayyana cewa daukacin kasashen duniya za su maida hankali kai,inda kasashen kowa zai fito ya bayyana halin da yake ciki game da ci gaban da ya samu wajen yaki da gurbatar muhalli, sannan kasashen za su bayyana dubarar da kowa ce kasa ta ke domin sauran kasashen na duniya su yi amfani da dubarun. Zamu duba batun yarjejeniyar samar da kudi biliyan daya wajen taimaka wa kan batun na gurbatar yanayi.
Tabarbarewar tsaro a kasashen yammacin Afirka zai ja hankalin MDD Shugaban zauren taron Farfesa Tijjani Muhammad Bande ya bayyana cewa "Akwai muhimman matakai kadda a manta da cewa shekaru biyu baya da suka wuce Majalisar Dinkin Duniya ta kai ziyara a wasu kasashen masu fama da matsalolin tsaro a yammacin Afirka musamman a Arewa maso gabashin Najeriya domin duba halin da yankin ake ciki. Akwai kuma batun tallafawa kasashen yankin tabkin Chadi da suka hada da ke yaki da aiyukan ta'addanciirinsu Kamaru da Najeriya da Nijar da Chadi Majalisar Dinkin Duniya na duba duk hanyoyyin da suka cancanta wajen tallafawa kasashen baki daya domin ganin sun tabbatar da tsaro.
Yunkurin MDD na sulhunta rikicin Gabas ta TsakiyaZarge-zargen mallaka da kera makamai na daga cikin abubuwan da ke kara hadasa tayar da jijiyoyin wuya tsakanin wasu kasashen na yankin Gabas ta Tsakiya, babban abinda Majalisar Dinkin Duniya za ta maida hankali in ji Farfesa Tijjani Muhammad Bande shi ne na kawo sulhu a tsakanin kasashen duk da yake wasu kasashen suna nuna turjiya to amma muna iyakacin kokarinmu saboda ita fitina an san farkonta amma ba a san karshenta ba.
Aiwatar da yarjejeniyar kula da 'yan gudun hijira Kasashen duniya a baya sun kulla wata yarjejeniya a Moroko da ke bai wa 'yan gudun hijirar ke fitowa cikakkiyar kulawa, kama daga inda suke fitowa da kasashen da suke biyowa har zuwa ga kasashen da suke samun mafaka domin tabbatar da hakin yan gundun hijira babban abinda muke jira shi ne na ganain kasashen sun aiwatar da ita wannan yarjejeniya.