1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TARON KUNGIYAR CINIKI TA DUNIYA A KASAR KENYA

Yahaya AhmedMarch 3, 2005

A birnin mombasan kasar Kenya, an fara wani taro na Kungiyar Ciniki Ta Duniya, wato WTO, wanda zai yi yunkurin cim ma daidaito a harkokin kasuwanci tsakanin kasashe masu arzikin masana'antu da kasashe masu tasowa.

https://p.dw.com/p/BwUv
Tutar Kungiyar Ciniki Ta Duniya.
Tutar Kungiyar Ciniki Ta Duniya.

Ministocin ciniki na kasashen duniya na halartar wani taron yini biyu a kasar Kenya don ba da kaimi a tattaunawar da ake yi tun da dadewa na cim ma yarjejeniyar daidaita harkokin cinikayya a duniya, karkashin sa idon Kungiyar Ciniki Ta Duniya, wato WTO.

Duk mambobi 148 na kungiyar na yunkuri ne na zartad da wasu muhimman kudurori kafin watan Yuli mai zuwa, don ganin cewa an sami ci gaba a taron nan na Doha, wanda ake kyautata zaton cewa, zai bunkasa tattalin arzikin duniya, da kuma rage yawan talaucin da dubu dubatan jama’a ke ta fama da shi a duniya.

Da yake yi wa wakilai jawabin bude taron, ministan ciniki na kasar Kenyan, Mukhisa Kituyi, ya bayyana fatarsa ta cewa kafin a kammala tattaunawar gobe, za a cim jma wata madafa, wadda za ta janyo dinke barakar da aka samu a tarukan baya da Kungiyar Ciniki ta Duniyar ta shirya.

A halin yanzu dai, an yi tsuru-tsuru ne ana jiran hukuncin da kotun daukaka kara na Hukumar Ciniki Ta Duniyar da ke birnin Geneva, za ta yanke game da karar da Amirka ta kawo a gabanta, inda take neman a soke wani hukuncin da aka yanke a cikin shekarar bara, wanda ya tabbatar cewa, ita Amirkan ta saba wa ka’idojin cinikayya na kasa da kasa da irin tallafin da take bai wa manoman auduganta. Kasar Brazil ce dai ta fara kai karar Amirkan gaban kotu kafin a yanke mata wannan hukuncin.

K

asashe masu tasowa dai na goyon bayan karar da Brazil ta dauka. Kamar yadda shugaban tawagar kasar Indiya a taron, Gopal Pillai, ya bayyanar:-

"Tallafin da Amirka ke bai wa maonman auduga, na gurgunta yunkurin da ake yi na samun adalci a kasuwar. Hakan kuma na janyo wa manoman Afirka da Asiya gagarumin cikas, saboda hakan na janyo musu faduwar farashi na audugar da suke noma."

Su ko kasashe masu ci gaban masana’antu na ganin cewa, idan Amirka ta sha kaye a kotun, hakan zai share fagen daukaka kararraki da kasashe masu tasowa za su yi ta dinga yi, game da tallafin da suke bai wa manomansu.

A cikin wannan hali na jayayyar dai, kasashe masu tasowa sun ce ba za su saduda ba, sai sun ga an nuna adalci a harkokin cinikayyar a kasuwannin duniya. Da yake jaddada hakan, jakadan kasar Benin a gun taron, Samuel Amehou, wanda kasarsa ke cikin muhimman kasashe masu sayad da auduga a kasuwannin duniya, ya ce:-

"Abin da kasashe masu tasowan ke sa ran samu a sabon taron da za a yi a kasar Hong Kong shi ne, wani sakamako wanda zai janyo soke tallafin da ake bai wa manoma a kasashe mawadatan."

Rashin jituwa tsakanin kasashe mawadata da kasashe masu tasowa a kan batun ba da tallafi ga manoma a kasashe masu arzikin masana’antun na barazanar janyo wargajewar tattaunawar, wadda aka fara tun shekara ta 2001. A cikin watan Yulin shekarar bara ne dai aka cim ma daidaito kan ci gaba da taron.

K

ungiyar Ciniki Ta Dunyar dai, na kyautata zaton cewa kasashen da ke halartar taron na Kenya, za su iya cim ma daidaito kan cinikayya a huskar ayyukan da ba na kere kere ba, wadda ta kai kashi 60 cikin dari na adadin harkokin cinikayya da ake yi a duniya baki daya. Wannan nau’in cinkayyar kuwa, ya kunshi fannoni ne kamarsu na kiwon lafiya, da ilimi da yawon bude ido.

A ce-ce ku cen da ake yi kuwa, kasashe mawadata na neman a rage harajin kwastam da ake dora wa kayayyakin da aka sarrafa a masana’antu ne idan aka shigo da su a kasashe masu tasowa. Saboda a nasu ganin, su ma suna nuna wa kayayyakin albarkatun noman da aka shigo da su daga kasashe masu tasowan, sassauci.

Su kuma kasashe masu tasowan, wadanda suka halarci taron na Kenya, suna kokarin kare maslaharsu ne na iya shigad da kayayyakin nomansu a kasuwannin duniya, kamar su Suga da sauransu.

Abin farin ciki a wannan taron dai, shi ne ganin cewa, muhimman kasashe masu ci gaban masana’antu kamarsu Amirka da Kungiyar Hadin Kan Turai da Japan, duk sun tura kusoshin jami’ansu zuwa birnin Mombasa a can kasar Kenya.