Taron ministocin kudin kasashen G7 a London
February 7, 2005A cikin wani jawabin da ya bayar gabanin taron na ministocin kudi na kasashen G7 da suka fi ci gaban masana’antu a duniya, tsofon shugaban kasar Afurka ta Kudu Nelson Mandela yayi kira garesu da su nuna halin sanin ya kamata su yafe wa kasashe masu tasowa dukkan bashin dake kansu. To sai dai kuma murna ta koma ciki a game da fatan da aka yi na cewar ministocin zasu cimma daidaituwa akan wani takamaiman shirin taimako ga kasashe masu fama da matsalar talauci. Amma duk da haka kasashen guda bakwai da suka fi ci gaban masana’antu a duniya, a karo na farko, sun bayyana yiwuwar yafe basusukan dari-bisa-dari. Bisa ta bakin sakataren baitul-malin Birtaniya Gordon Brown, ministocin kudin na kasashen G7 sun bude wani sabon babi na tarihi a lokacin taron nasu na birnin London. Domin kuwa wannan shi ne karo na farko da aka yi batu a game da yafe basussuka a cikin wata sanarwar bayan taron kasashen G7. Wannan babban ci gaba ne akan hanyar warware wasu matsalolin da suka dade suna ci wa jama’a tuwo a kwarya, wanda kuma ya bayyanar a fili cewar rashin adalci ba abu ne mai dorewa har abada ba, in ji sakataren baitul-malin Birtaniyar. A hakika kuwa wadannan basusukan sune ummal’aba’isin dankwafewar da yawa daga cikin kasashe masu tasowa. A halin yanzu haka yawan bashin bankin duniya da asusun bayar da lamuni na duniya dake kan kasashe masu tasowa ‚yan rabbana ka wadata mu ya kai dalar Amurka miliyan dubu tamanin. Shi dai sakataren baitul-malin Birtaniya Gordon Brown, ko da yake yayi bakin kokarinsa, amma bai cimma nasarar shawo kan dukkan ministocin kudi na kasashen G7 da gwamnonin manyan bankunansu domin su yafe wa kasashe masu tasowa dukkan bashin dake kansu ba. A maimakon haka, a cikin sanarwar bayan taron, sai aka yi batu a game da bin matsalolin kasashen a wawware ta yadda za a iya yafe wa wasu daga cikinsu illahirin basussukan dake kansu. Kazalika ministocin ba su yi na’am da shawarar da Birtaniya ta bayar ba na ribanya yawan taimakon da ake ba wa kasashe masu tasowa. Duka-duka dai maganar yafe daukacin bashin shawara ce Birtaniya ta bayar, wacce kuma ministocin na kudi ba zasu iya yanke hukunci akanta ba, sai dai su kansu shauagabannin kasashen na G7 a lokacin taron kolinsu da zasu gudanar a Gleneagles ta kasar Scottland.