Taron Ministocin Turai a kan Siriya
May 27, 2013Cece-ku-ce dangane da yiwuwar taimaka wa 'yan tawayen Siriya da makamai, shi ne zai kasance babban ajandar taron ministocin harkokin waje na Kungiyar Tarayyar Turai da zai gudana a wannan Litinin a birnin Brussels. Wannan taron na zuwa ne a daidai lokacin da takunkumin da EU din ta kakaba wa Siriya kan shigar da makamai kasar ke karewa a ranar daya ga watan Yuni. Wannan takunkumin dai kazalika ya shafi 'yan tawayen, wanda kuma ke bukatar fadada shi idan har za a taimaka musu da makamai. Birtaniya dai ta dage ganin cewar an taimaka wa 'yan tawayen da makamai, a yayin da mafi yawan sauran kasashen Turai ke adawa da wannan yunkuri. A ganinsu dai, hakan tamkar kara ingiza rikicin kasar ne. Majiyar diplomasiyya a wurin taron na nuni da cewar, har yanzu babu masaniya dangane da ko ministocin Turan za su cimma fadada takunkumin haramta shigar da makamai Siriya ko kuma a'a. A yanzu haka dai gwamnati a Damaskus ta ce a shirye take ta halarci taron kasa da kasa da ake shirin gudanarwa domin neman mafita kan rikicin kasar. Ministan harkokin wajen kasar Walid Muallem ya tabbatar da haka a wata ziyara da ya kai birnin Bagadazan kasar Iraki.
Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasiru Awal